✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ballon d’Or: ’Yan wasa 30 da ke sahun zama gwarzon dan wasan duniya

Akwai ’yan wasa 30 da ke kan sahun gaba wajen lashe kyautar Balon d’Or a bana.

A halin yanzu akwai ’yan wasa 30 wanda tauraruwarsa ke ci gaba da haskawa a bana kuma suke kan sahun gaba wajen lashe kyautar gwarzon dan wasan shekara ta Ballon d’Or.

Mujallar Kwallon Kafa ta Faransa, France Football ce ta fitar da jerin ’yan wasa 30 da a cikinsu daya zai lashe kyautar Ballon d’Or ta shekarar 2021.

Mujallar wacce ta fitar da kididdigar a karshen makon da ya gabata, ta yi la’akari da bajintar ’yan wasan a gasanninsu na gida da kuma na nahiyya, gami da gasar Euro 2020 da ta Copa America, inda har a yanzu zaratan ’yan kwallon ke ci gaba da nuna kansu.

Ana iya tuna cewa, a bara wanda ya kasance karon farko a tarihi, ba a bayar da da kyautar zakaran dan kwallon kafa na duniya ba, saboda annobar Coronavirus.

France Football wadda ke bayar da kyautar Ballon d’Or duk shekara, ta ce babu yadda za a yi adalci wajen bayar da kyautar a bara ganin cewa akwai wasu kasashen da ba su kammala gasarsu ba.

Sai dai tun a baran Mujallar ta ce za ta mayar da hankali ne wajen shirya bikin da za a gudanar na bayar da kyautar a bana.

Dan wasan Argentina da ke murza leda a PSG, Lionel Messi ne ya lashe kyautar ta karshe da aka bayar a shekarar 2019, a yayin da Megan Rapinoe ta Amurka ta lashe kyautar a bangaren mata.

Kodayake, sai a watan Nuwamba za a gabatar da kyautar ta bana, inda bajintar da ’yan wasan za su nuna a makonni masu zuwa ita ce za ta taka rawar gani wajen yanke hukunci a yayin fidda gwarzon dan wasa na bana.

’Yan jaridu daga kasashe daban-daban da masu horaswa da kuma kyaftin-kyaftin ne dai ke suke jefa kuri’a wajen zaben dan wasan da zai lashe kyautar.

Bayanai sun ce za a gudanar da bikin bayar da kyautar ne a ranar 29 ga watan Nuwamba a birnin Paris na kasar Faransa.

Ga dai jerin ’yan wasa 30 da France Football ta fitar tare da kungiyoyi da kuma kasashen da kowane dan wasa ya fito:

Riyad Mahrez (Manchester City/Masar)
N’Golo Kante (Chelsea/Faransa)
Erling Haaland (Borussia Dortmund/Holland)
Leonardo Bonucci (Juventus/Italy)
Mason Mount (Chelsea/Ingila)
Harry Kane (Tottenham/Ingila)
Gianluigi Donnarumma (PSG/Spain)
Karim Benzema (Real Madrid/Faransa)
Raheem Sterling (Man City/Ingila)
Nicolo Barella (Inter Milan/Italy)
Lionel Messi (PSG/Argentina)
Bruno Fernandes (Manchester United/Portugal)
Pedri (Barcelona/Spain)
Luka Modric (Real Madrid/Croatia)
Giorgio Chiellini (Juventus/Italy)
Kevin De Bruyne (Manchester City/Belgium)
Neymar (PSG/Brazil)
Ruben Dias (Manchester City/Portugal)
Lautaro Martinez (Inter Milan/Argentina)
Simon Kjaer (AC Milan/Denmark)
Robert Lewandowski (Bayern Munich/Poland)
Jorginho (Chelsea/Italy)
Mohamed Salah (Liverpool/Masar)
Cesar Azpilicueta (Chelsea/Spain)
Romelu Lukaku (Chelsea/Belgium)
Cristiano Ronaldo (Manchester United/Portugal)
Gerard Moreno (Villarreal/Spain)
Phil Foden (Manchester City/Ingila)
Kylian Mbappe (PSG/Faransa)
Luis Suarez (Atletico Madrid/Uruguay)