✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ban ce a hana Buhari zuwa asibiti a kasar waje ba —Sanata La’ah

Sanata La'ah ya karyata rahoton cewa ya bukaci a hana Buhari zuwa asibiti a kasar waje.

Shugaban kwamatin Raba Daidai na Majalisar Dattawa, Sanata Danjuma Laah, ya musanta rahoton da aka alakanta da shi, cewa ya bukaci a hana Shugaba Buhari tafiya kasashen wajen neman magani. 

Sanata La’ah ya ce shi dai ya bukaci a inganta Asabitin Fadar Shugaban Kasa da duk abun da ya kamata ta yadda asibitin zai iya ba Shugaban Kasa da manyan jami’an gwamanti kulawar da ta dace ba sai sun je kasar waje ba.

“Babu wanda na bukaci ya dakatar da Buhari daga tafiya duba lafiya kasashen waje”, kamar yadda La’ah ya shaida wa ’yan jarida.

Rahotannin da La’ah ke musantawa sun ambato shi yana bayani ne yayin da Babban Sakataren Fadar Shugaban Kasa, Tijani Umar, ke kare kasafin 2021 a gaban kwamatin.

Umar, ya gabatar da kasafin biliyan N19.7 wanda daga ciki aka ware Naira biliyan 1.3 don kulawa da inganta asibitin Fadar Shugaban Kasa.

Rahotannin sun ce kwamitin La’ah ya amincewa da kasafin ne bisa sharadin ba za a bar Shugaban Kasa ya je kasar waje neman magani ba.