✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ban ga amfanin rayuwar Shekau ba – Mahaifiyarsa

Ta ce sai da ta shafe shekara 15 ba ta sa shi a idonta ba.

Mahaifiyar tsohon Shugaban kungiyar Boko Haram, marigayi Abubakar Shekau, wato Falmata Modu ta ce sam ba ta ga amfanin rayuwar haihuwarsa ba.

Ta bayyana hakan ne a cikin wata zantawarta da gidan Talabijin na Trust TV, mallakin kamfanin Media Trust.

Falmata wacce ta yi magana a cikin harshen Barbanci ta ce, “Ni ban san dadinsa ba, sam ban ga iyalansa ba, babu abin da zan ce ko ya mutu ko bai mutu ba, duk daya ne a wajena, domin babu wani amfani da ya yi min a rayuwa, wannan kuma sai a Lahira.

Latsa nan don kallon kadan daga cikin tattaunawarmu da ita

“Ban taba sanin ya haihu ko bai haihu ba, gaskiya ya cutar da rayuwata,” inji ta.

Da aka tambayeta ko tana son shi a matsayinta na mahaifiyarsa sai ta ce duk uwa tana son danta ko me ya zama, sai dai ta yi Allah-wadai da halin da ya shiga.

Shekau dai shi ne danta na farko, amma dai ta ce ba za ta ce ta ji dadin haihuwarsa ba, domin ta shafe fiye da shekara 15 ba ta sa shi a idonta ba, don haka ita mutuwarsa ta fi mata.

“Ban san iyalansa balle in ga ’ya’yansa, amma dai idan suna nan Allah Ya raya su, sai dai gaskiya ina takaicin kasancewa uwa ga dan da ya jefa dubban jama’a a cikin damuwa,” inji Falmata.

Za ku iya kallon cikakken shirin talbijin din kan rayuwar Shekau da matsayin mahaifiyarsa da ’yan uwansa a kansa, a tashar Trust TV, 164 StarTimes da kuma shafin Facebook da YouTube na Daily Trust.