✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ban ga laifin masu barin Najeriya don neman ingantacciyar rayuwa ba —Kakakin Buhari

“Ga duk mutum dayan da ya tafi, akwai darinsa da za su zauna.”

Mai Magana da Yawun Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, Femi Adesina, ya ce bai ga wani abin tayar da jijiyoyin wuya ga ’yan Najeriyar da ke son barin kasar don neman ingantacciyar rayuwa ba.

Ya bayyana haka ne yayin tattaunawarsa da gidan talabijin na Channels a cikin shirinsu na Sunday Politics, wanda ya mayar da hankali kan nasarorin da gwamnati mai ci ta samu tun bayan darewarta karagar mulki a 2015.

Sai dai ya ce bai kamata a zargi gwamnatin Buharin ba kan yadda matasan kasar ke yin tururuwar barin kasar, wacce suke yi wa lakabi da ‘Japa’.

“Idan mutum yana tunanin cewa yin hijira ita ce ta fi masa, sai mu ce Allah Ya raka taki gona. Amma bai kamata ka ce tafiyar na nuna cewa akwai matsala a kasar ba,” inji shi.

Ya kuma ce duk da yake mutane na barin Najeriya tun kafin zuwan gwamnati mai ci, akwai wadanda ko wanne yanayi aka shiga ba za su bar kasar ba.

A cewarsa, “Ka ce mutum 70,000 sun bar Najeriya, kaso nawa ke nan a cikin mutum miliyan 200?

“Akwai fa mutanen da ko wanne yanayi kasar nan ta tsinci kanta ba za su taba barinta ba. Ga duk mutum dayan da ya tafi, akwai darinsa da za su zauna,” inji shi.

Dangane da batun satar danyen mai a kasar kuwa, Femi Adesina ya ce da zarar sun kammala bincike za su gurfanar da duk wani mai hannu a cikin aika-aikar a gaban kuliya.