✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ban ga wanda ya fi ni gogewa a harkar mulki ba —Tinubu

Tinubu ya ce yana da gogewa a harkar mulki fiye da kowane dan Najeriya.

Jagoran Jam’iyyar APC na Kasa, Bola Tinubu, ya ce zai yi takarar shugaban kasa ne saboda ya fi kowane dan Najeriya kwarewa a harkar shugabanci.

Tinubu wanda tsohon gwamnan na Jihar Legas ne, ya bayyana haka ne a Ado-Ekiti a wata tattaunawa da sarakunan gargajiya na Jihar Ekiti.

Jagoran na APC na kasa ya ce Najeriya na matukar bukatar shugaban da zai hada kan jama’a, ya magance matsalar rashin tsaro da kuma kawo cigaban rayuwa da tattalin arzikin yadda ya kamata.

Ya ce ya ziyarci sarakaun gargajiyar ne don neman shawarwarinsu game da takararsa a 2023 da kuma samun fata na gari daga gare su a matsayinsu na iyayensa kasa.

Tinubu, ya ce ya yanke shawarar ganawa da sarakunan ne saboda girmama al’ada da da tarihi.

“Mun yi gwagwarmayar tabbatar da dimokuradiyya kuma a yau muna da dimokradiyya amma har yanzu ba mu da kwanciyar hankali.

“Ya kamata mu samu kyakkyawan tsarin noma ta yadda sauran kasashe za su sayi abin da mu ke nomawa.

“Mun zabi dimokuradiyya don haka bai kamata mu yi kasa a gwiwa ba wajen samar wa yaranmu yaruwa ta gaba mai inganci.

“Domin Najeriya ta tsaya tsayin daka ta kuma bunkasa, muna bukatar hakuri da juriya. Dole ne mu samu hadin kai, ta haka ne kadai za mu iya zama tsintsinya madaurinki daya. Shi ya sa muka kafa APC da wannan manufa.

“Ina so in shaida muku cewa Najeriya na bukatar canji sosai. Na san yadda Legas ta kasance a baya a lokacin da na karbi mulki kuma ba mu taba faduwa a zabe ba,” a cewar Tinubu.

Ya ce dole ne a samar da shugabanci na gari don saita Najeriya ta hau tudun turbar tsira.

“Ni ne gwamna na farko a Najeriya da ya fara biyan kudin WAEC ga daliban sakandare. Zan sake aikata hakan idan na zama shugaban kasa,” inji shi.

Tinubu, ya ce a harkar siyasa ko mulki shi ba bako ba ne, don haka shi ne mutum da ya fi cancata ’yan Najeriya su bai wa amanar kasar, sakamakon yadda ya shafe shekara 70 yana hidimta wa gwamnati.

“Na yi tafiya tare da MKO Abiola a SDP, ni ne Sanata mafi karancin shekaru a wancan lokacin.

“Mun yi imanin cewa dole ne a samu dimokuradiyya a Najeriya, dole ne a samu ’yanci da kuma damarmaki ga ’yan kasa.

“Dole ne mu hada kai, mu tallata kanmu, maimakon fada. Dukanmu muna ganin abin da ke faruwa a Ukraine a yau, ba ma bukatar irin hakan ta faru a Najeriya,” inji shi.

A nasa jawabin, Sanata Dayo Adeyeye, wanda shi ne shugaban yakin zaben Tinubu a Kudu Maso Yamma, ya ce Najeriya na bukatar shugaba mai kwarewa irin Tinubu.

“Tinubu ya yi wa Jihar Ekiti halarci, ya nada ’ya’yanta kwamishinoni da mukaman siyasa da dama lokacin da yake gwamnan Legas.

“Tinubu ya karrama gwarzonmu, Adekunle Fajuyi ta hanyar gina masa gida. Ya taimaki mutane da yawa, ciki har da ni.

“Tinubu ya kawo sauyi ga shugabanci a Legas. A gaskiya mutum ne wanda babu irinsa.”

Da yake mayar da martani, Oba Gabriel Adejumo, Onisan na Isan-Ekiti kuma Shugaban Majalisar Sarakunan Ekiti, ya ce kundin tsarin mulki ya bai wa duk wani dan Najeriya da ya cancanta damar neman takarar kowane mukami.

Ya yi addu’ar Allah Ya yi wa Tinubu jagora kan cikar burin nasa.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ya rawaito cewa Tinubu ya samu rakiyar Mataimakin Gwamnan Jihar Ekiti, Bisi Egbeyemi da mambobin kungiyar SWAGA daga kananan hukumomi 16 na jihar.