✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ban gamsu da sakamakon zaben Anambra ba, kotu zan tafi – Dan takarar APC

“INEC ta hada baki da Gwamna da jami’an tsaron wajen yi wa dan takararmu magudi.

Dan takarar jam’iyyar APC a zaben Gwamnan Jihar Anambra na ranar Asabar, Sanata Andy Uba, ya yi watsi da sakamakon zaben da Hukumar Zabe ta Kasa Mai Zaman Kanta (INEC) ta sanar.

Aminiya ta rawaito cewa dan takarar jam’iyyar APGA, Farfesa Charles Soludo, wanda ya sami kuri’a 112,229 ne INEC ta ayyana a matsayin wanda ya lashe zaben.

Dan takarar PDP, Valentine Ozigbo ne ya zo na biyu da kuri’a 53,807, yayin da shi kuma Sanata Andy ya sami kuri’a 43,285.

To sai dai a cikin wata sanarwa a Abuja ranar Alhamis ta bakin kakakin yakin neman zabensa, Ambasada Jerry Ugokwe, Sanata Andy ya ce zai garzaya kotu don kwato hakkinsa.

Sanarwar ta ce, “Sakamakon zaben nan akwai magudi a cikinsa, kuma bai dace da zabin mutanen Anambra ba.

“INEC ta hada baki da Gwamna Willie Obiano da jami’an tsaron da aka turo Jihar, inda suka yi wa dan takararmu kwanta-kwanta.

“Zaben cike yake da kura-kurai, tsoratar da masu zabe da kuma yin amfani da haramtattun hanyoyi wajen yin karfa-karfa.

“Ta yaya za a ce dan takararmu, wanda ya samu kuri’a sama da 200,000 a zaben fid da gwani na APC zai tsira da kuri’a 43,000 da dan wani abu? Wannan hankali ba zai dauka ba.

“Akwai mamaki matuka a ce APGA, jam’iyyar da aka rika turuwar barinta, ciki har da Mataimakin Gwamna, a ce ta lashe wannan zaben.

“Muna kira ga magoya bayanmu su kwantar da hankulansu, amma za mu bi dukkan hanyoyin da doka ta tanada wajen ganin mun kwato hakkinmu,” inji sanarwar.