✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ban gamsu da shirin gyara halin tubabbun ’yan Boko Haram a Gombe ba – Gwamna

Gwamnan ya ce kamata ya yi a mayar da su Jami'ar Sojoji da ke Biu.

Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya na jihar Gombe ya ce bai gamsu da yadda sansanin ’yan yiwa kasa hidima da ke Malam Sidi a Karamar Hukumar Kwami ke ci gaba da zama sansanin gyaran hali ga tubabbun ’yan Boko Haram ba.

Ya ce amfani da sansanin ya jefa al’umma cikin fargaba saboda daga na wucin gadi har an shekara  shida.

Gwamna Yahaya ya ce kamata ya yi a ware musu wuri na musamman a Jami’ar Sojoji da ke Biu a Jihar Borno don aikin gyaran halin.

Ya bayyana hakan ne a lokacin da ya karbi bakuncin babban kwamandan Rundunar Sojoji ta Operation Safe Haven,  Manjo Janar Ibrahim Ali, a gidan gwamnatin Jihar da ke Gombe ranar Alhamis.

Ya ce koka cewa kusan duk wadanda ake kawowa ba ’yan asalin Jihar ba ne, don haka bai kamata a sa Jihar ta sha wahala wajen daukar irin wannan dawainiyar ba.

A cewarsa, sansanin ya karbi bakuncin daruruwan tubabbun ’yan kungiyar ta Boko Haram daga sassa daban-daban na yankin Arewa maso Gabas, da ma wasu Jihohin kasar nan.

Gwamnan, ya kara da cewa tun asali sansanin wuri ne da gwamnatin Jihar Gombe ta kashe magudan kudi ta gina wa masu yi wa kasa hidima a matsayin sansaninsu, amma yanzu shekara shida tana karbar ’yan Boko Haram a wajen.

Gwamna Yahaya ya ce da farko an tsara amfani da sansanin ne na wucin gadi tsawon wata shida, amma yanzu batun ya zarce yana so ya zama na dindindin, inda ya ce gwamnatinsa ba za ta iya ci gaba da kula da aikin ba.