✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ban iya turanci ba- Adam Zango

Fitaccen dan wasan Hausa, Adam A. Zango ya ce mutane su daina masa gyaran turanci domin ba yaransa bane. Adam Zango ya bayyana haka ne…

Fitaccen dan wasan Hausa, Adam A. Zango ya ce mutane su daina masa gyaran turanci domin ba yaransa bane.

Adam Zango ya bayyana haka ne a wani faifan bidiyo da ya wallafa, inda yake cewa “Me ya sa mutane suke auna fahimtata da Turanci? Shin na taba fada ma wani cewa na je makaranta ne? ko turancin da nake yi ma a titi na koya.

Zango ya kara da cewa shi bai iya turanci domin shi dan fim din Hausa ne, “Ina yin fim di Hausa ne, kuma ina waka ne da harshen Hausa. Turancin da nake yi ma kawai ina yi domin masoya na da ba sa jin Hausa. Abin da na sani kawai shi ne na samu nasara a rayuwa,” in ji Zango.