✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ban ji dadin abin da PSG ta min ba —Mbappe

Paris Saint-Germain ta ki amincewa ta sayar da dan wasan gabanta, Kylian Mbappe, ga Real Madrid a lokacin cinikayyar ’yan wasa duk da cewa dan…

Paris Saint-Germain ta ki amincewa ta sayar da dan wasan gabanta, Kylian Mbappe, ga Real Madrid a lokacin cinikayyar ’yan wasa duk da cewa dan wasan ya nuna sha’awarsa na barin kungiyar.

Amma Mbappe ya hakura tare da ci gaba da zama a PSG duk da cewa burinsa na barin ta bai cika ba, kamar yadda ya bayyana a tattaunawarsa da RMC Sport.

“Na sanar da su cewa ina son tafiya, shi ya sa na ki sabunta kwantaragina.

“Na so a ce kungiyar ta samu wasu kudade a cinikayyar da za ta iya amfani da su ta sayi wanda zai maye gurbina.

“Tun tuni na sanar da su cewa ina son tafiya, amma suka ki yin komai a kai. Duk da haka ina fatan dukkaninmu za mu amfana a gaba.

“Gaskiya ban yarda cewa sai ranar karshe ta cinikayyar ’yan wasa ba sannan za a ce za kammala komai.

“Ina nan a kan bakata, na bayyana ra’ayina tun tuni kuma na fada a kan lokaci.

“Amma zan girmama shugabannin wannan kungiya idan ba su so na tafi zan zauna,” a cewar Mbappe.