✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ban kai ga yanke shawara kan sauya sheka ba — Shekarau

Sai dai ya ce yana ci gaba da tuntuba da tattaunawa a kan lamarin

Tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma Sanata mai wakiltar Kano ta Tsakiya a Majalisar Dattawa, Ibrahim Shekarau ya ce bai kai ga yanke shawara kan ficewa daga jam’iyyar APC ba.

An dai fara rade-radin cewa Sanatan da wasu manyan ’yan siyasa a Jihar sun kammala shirye-shiryen ficewa daga APC zuwa jam’iyyar NNPP mai alamar kayan marmari.

Hakan na zuwa ne bayan harsashen da ake yi cewa ba lallai ne Shekarau ya sake samun takarar ba a APC sakamakon rikicin Shugabancin da tsagin su ya tafka da na Gwamnan Jihar, Abdullahi Umar Ganduje.

To sai dai a hirar shi da Aminiya ta wayar salula, mai magana da yawun tsohon Gwamna Shekarau, Dokta Sule Ya’u Sule, ya ce, ba su kai ga yanke shawarar ficewar ba tukunna.

A cewar shi, “Gaskiya ba wai an koma ba ne, akwai wasu abubuwa da muke ta tattaunawa a kai.

“Yanzu haka akwai taron da muke yi, amma gaskiya ba a dauki wata matsaya ba tukunna.

“Dole sai bayan wadannan tarukan da tattaunawar za a yanke hukunci, amma yanzu dai muna cikin jam’iyyar APC,” inji Dokta Sule.

Sauran wadanda ake rade-radin ficewar tasu daga APC sun hada da tsohon Shugaban Marasa Rinjaye na Majalisar Wakilai, Sulaiman Kawu Sumaila, da tsohon Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kano kuma dan majalisar tarayya mai wakiltar Rano/Kibiya/Bunkure, Kabiru Alhassan Rurum.

Ko a makon da ya wuce dai mambobin Majalisar Dokokin Jihar Kano su tara sun sauya sheka da jam’iyyar PDP zuwa NNPP, wacce ke karkashin jagorancin tsohon Gwamnan Jihar, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso.