✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ban mutu ba, dogon suma na yi – Ummi Zee-zee

A cewarta, "Ina mai ba ku hakuri dangane da labarin da kuka ji cewa na mutu. To da raina ban mutu ba.”

Tsohuwar jarumar masana’antar Kannywood, Ummi Zee-zee ta bayyana cewa tana raye ba ta mutu ba.

A makon jiya ne aka shiga rudu da mamaki biyo bayan samun labarin cewa ta rasu, labarin da tun farko ya fito daga shafinta na Instagram.

Sai dai tsohuwar jarumar ta ce ta yi dogon suma ne, wanda hakan ya sa kawarta wadda a lokacin tana gidanta ne ta yi tsammanin ta rasu bayan ta yi ta zuba mata ruwa amma ba ta farfado ba.

A cewarta, “Ina mai ba ku hakuri dangane da labarin da kuka ji cewa na mutu. To da raina ban mutu ba.

“Kawai dai na yanke jiki na fadi ne a gidan wata kawata a Kaduna.To sai ta yi zaton na mutu ne saboda ta yi ta zuba min ruwa ban farfado ba.

“Shi ya sa ta bayyana wa duniya cewa na mutu sai da mijinta ya kaini asibiti ne aka duba, aka ce ban mutu ba.

“Saboda haka duk wanda ya nuna damuwarsa jin labarin, ina godiya da kaunarsa. Sai dai ina fama da rashin lafiya matuka domin ina fama da ciwon matsananciyar damuwa. Don haka ina bukatar addu’ar masoya,” inji Zee-Zee.

‘Wasan dirama take yi’

Sai dai kuma a kasan wannan rubutun, darakta Aminu S. Bono cewa ya yi, “Zango na uku ke nan, saura zango na hudu.”

Shi ma Darakta Sheikh Isa Alolo ya tofa albarkacin bakinsa, inda ya ce, “Abin mamaki shi ne ita da take rude amma ba ta manta lambobin sirrin wayarki ba, shi ne ta bude wayarki ta shiga Instagram dinki ta yi rubutun, maimakon ta yi a nata shafin. Ko da yake ba abin mamaki ba ne ko ita ba ta da shafin Instagram. Allah Ya kare mu, Ya kare mana imaninmu,” inji shi.

Kusan mako biyu kenan ana tattauna batun Ummi Zee-zee tun bayan da ta fito ta sanar da cewa za ta kashe kanta, inda daga bisani ta bayyana cewa damfararta aka yi Naira miliyan 450 sannan ta rasa saurayinya da kuma mahaifinta.

Aminiya ta kuma ruwaito inda jarumar ta sake tada kura, inda take godiya da masoyanta bisa nuna mata kauna da suka yi, inda a cikin bayanin ta bayyana cewa Kiristoci sun fi Musulmi tausayi.

A shekarun baya, Ummi Zee-zee ta taba jawo cece-kuce inda ta fito ta bayyana cewa tana soyayya da mawakin Kudu mai suna Timiya.

Sai dai daga bisani ta bayyana cewa babu abun da take da-na-sanin aikatawa a duniya sama da soyayyarta da mawakin, wanda ko a lokacin shima an zarge shi da damfararta wasu kudade.