✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ban san yawan mutanen da na kashe ba – Yaron Bello Turji da ya shiga hannu

Ya ce duk lokacin da suka kai hari, ana ba su tsakanin N20,000 zuwa N30,000.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Katsina ta kama wani matashi mai suna Naziru Sani, daya daga cikin yaran kasurgumin dan bindigar nan da ya addabi Jihohin Arewa maso Yamma, wato Bello Turji.

Sai dai matashin ya ce ba zai iya faden adadin mutanen da ya taba kashewa ba yayin ayyukan nasu a sassa daban-daban.

Matashin, mai kimanin shekaru 25 dai mazaunin garin Makera ne a Karamar Hukumar Tsafe ta Jihar Zamfara.

Rundunar ta gabatar da Naziru ne ga manema labarai a hedkwatarta da ke Katsina ranar Litinin.

Matashin ya ce bai san iya yawan mutanen da ya kashe ba a lokuttan da suke kai hare-haren su.

Sai dai kamar yadda ya ce, duk lokacin da aka kai hari ana ba su N20,000 zuwa N30,000.

Naziru dai ya shiga hannu ne a lokacin da yake kan hanyar shi ta zuwa Jihar Neja wajen mahaifinsa, kamar yadda ya ce.