✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ban taba cewa zan rushe masarautun Kano ba – Abba Gida-gida

Ya ce hasali ma yana da kyakkyawar dangantaka da su

Zababben Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya ce bai taba furta cewa zai rushe wani gini a Jihar ko kuma rushe masarautun da gwamnati mai barin gado ta kirkiro ba.

Ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa ta kai tsaye da ya yi da RFI ta shafinsu na Facebook ranar Talata.

Sai dai ya ce akwai wani zama na musamman da kwamitocin da za su kafa zai duba bukatun al’ummar Jihar daba-daban cikin watanni uku na farkon mulkinsa, wanda da shi ne za su yi aiki.

Ya ce, “Tun da na fara kamfe na zagaya Kananan Hukumomi 44, kuma kusan ni ne kadai dan takarar da ya je Kananan Hukumomin duka ya gabatar da kudurorinsa.

“Kuma duk inda na je ina gabatar da kudurorin da za su taimaki al’umma, amma ba a taba ji na ce zan rushe wani guri ko zan kori wasu sarakuna ba.

“Hasalima ni kadai ne da duk Karamar Hukumar da idan na je da Sarki sai na je na kai masa ziyara na gabatar masa da kaina, idan kuma Hakimi ne sai an tara min Dagatai da malamai na fada musu manufofina.

“Saboda haka shaci fadi ne kawai zancen, kuma duk wadanda ka ji suna wannan cece-kucen, to suna da guntun kashi a tattare da su, mutane ne wadanda watakila su ne suka hada baki da azzalumai suka yi abinda bai kamata ba.

“Mu kuma gwamnatinmu duk wanda ya san cewa ya yi aiki daidai yana da gaskiya ta ya je ya hau gadonsa ya yi barci, babu abin da zai same shi,” in ji shi.

Abba ya kuma ce duk wanda ya san ya yi harambe ko ya danne dukiyar al’umma, ya tabbatar yana da shiri, domin kwana da sani cewa ba za su kyale shi ba.