Ban taba cin bashi ba a lokacin da nake gwamna —Kwankwaso | Aminiya

Ban taba cin bashi ba a lokacin da nake gwamna —Kwankwaso

Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, Tsohon Gwamnan Jihar Kano
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, Tsohon Gwamnan Jihar Kano
    Abubakar Muhammad Usman da Abdullateef Salau

Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana cewa bai taba ciyo bashi ba lokacin da ya yi gwamnan jihar na tsawon shekara takwas.

Sanata Kwankwaso ya bayyana haka ne a wata tattaunawa da aka yi da shi a gidan talabijin na ARISE a ranar Juma’a.

Kwankwaso ya soki Gwamnan Jihar Kano mai ci, Abdullahi Umar Ganduje, kan jefa jihar cikin kangin bashi, babu gaira, babu dalili.

A cewarsa, ana bin Kano bashin kudi da ya kai biliyan N187, abin da ya ce hakan babban kuskure ne a bari ya ci gaba da faruwa.

Kwankwaso wanda shi ne jagoran tafiyar siyasa ta Kwankwasiyya, ya ce dukkanin ayyukan da gwamnatin jihar ke yi a yanzu, ana aiwatar da su ne ta hanyar ciyo bashi, wanda kuma babu bukatar hakan.

“A Kwankwasiyya, ba mu yarda da ciyo bashi ba, sai dai idan cin bashin ya zama dole, don haka zan iya cewa tun daga 1999 zuwa 2003 ban taba ciyo bashi daga cikin gida ko kasashen ketare ba.

“Amma kuma sai da muka biya dukkannin bashin da gwamnatin dana gada ta ciyo.

“Sannan da na sake dawowa a 2011 mun sake samun tarin bashi, akwai bashin da muka tarar na Dala miliya 200 da aka ciyo daga Bankin Duniya, wanda ya shafi yaki da cutar maleriya,” inji shi.