✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ban taba faduwa zabe ba a rayuwata — Tinubu

Tinubu ya ce ba ya tsoron kara wa a zaben 2023 saboda yana da goyon Shugaba Buhari.

Dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu, ya bigi kirjin cewa tun da yake bai taba faduwa zabe ba.

Tinubu ya yi wannan kalami ne a matsayin martani ne don sukar tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Babachir Lawal, kan kalamansa na baya-bayan nan a kan cewar ba lallai ya iya lashe zaben 2023 ba.

Kwanan nan, Babachir ya kalubalanci Tinubu kan lashe zaben Shugaban Kasa a 2023.

Babachir ya ce Tinubu ba zai iya lashe zaben Shugaban Kasa a 2023 ba sakamakon tikitin takarar Musulmi da Musulmi da jam’iyyar APC ta yi.

Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, ya yi ikirarin cewa mai rike da tutar jam’iyyar APC, ya raina Kiristocin Arewa ta hanyar zabar Musulmin da zai yi masa Mataimaki.

Sai dai da yake mayar da martanin, Tinubu ya bayyana kalaman na Babachir a matsayin gajen hakuri.

Tinubu ya yi magana ne ta bakin daraktan yada labarai na kwamitin yakin neman zabensa, Bayo Onanuga.

Ya jaddada cewa kalaman Babachir hasashe ne kuma abin dariya.

Ya ba da tabbacin cewa ya dauki hanyar samun gagarumar nasara a zaben shugaban kasa mai zuwa.

Tinubu ya ce zai lashe zaben shugaban kasa ne da goyon bayan jam’iyyar APC da kuma Shugaban Kasa Muhammadu Buhari.

Asiwaju ya bayyana cewar falan-daya yake yi a zabe, inda ya ce bai taba shiga zaben ya fadi zabe ba.

Jihohi 22 ne ke karkashin jam’iyyar APC mai mulki, wanda jam’iyyar ke sa ran za ta iya samun nasarar lashe zaben 2023 da kw tafe.

“Babachir ya fara tunkarar rarrabuwar kawuna da ke kungiyarsa, maimakon bayyana sakamakon zabe.

“Wannan mutumin, wanda ke kokarin kawo rarrabuwar kai, dan Karamar Hukumar Hong ne daga Jihar Adamawa. Ya gaza samar wa Buhari mazabarsa a zaben 2019, duk da cewa muna da Kirista da yawa da suka zabi Buhari,” inji shi.