✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ban tsayar da wanda zai gaje ni ba — Gwamna Ganduje

Sabani rade-radin da ake yi, Ganduje ya ce bai tsayar da kowa ba tukunna.

Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya ce bai tsayar da wanda zai gaje shi ba a matsayin Gwamna bayan kammala wa’adinsa a 2023. A cikin tattaunawarsa da Aminiya, Ganduje ya tabo batutuwa siyasa da dama, ciki har da dalilin da ya sa Gwamnoni ba sa saka hannu a zartar da hukuncin kisa ga wadanda kotu ta yanke musu hukunci.

Kasancewar ka fara siyasa tun a Jamhuriyya ta Biyu, sannan ga ilimin zamani da sanin makamar aiki a matsayinka na ma’aikacin gwamnati, shin kana tunanin akwai wani wanda ya fi ka shiri wajen fitowa takarar Gwamnan Jihar Kano?

Babu Shakka na shiga siyasa tun farkon farin dimokaradiyya a Najeriya, wanda ma har na fito takara a lokacin a Jam’iyyar NPN, amma ban yi nasara ba. Kowa ya san cewa a wancan lokaci  mutanen Kano ba su da wata jam’iyya da suke so irin Jam’iyyar PRP ta Malam Aminu Kano.

A lokacin ina matsayin malami inda nake koyarwa a Jami’ar Bayero da ke Kano, sai na ga ai ya dace ni ma in fto domin a yi gwagwarmayar siyasar hamayya da ni, kuma hakan ya ba ni kwarin gwiwa har na fito takara, duk da na san cewa ba zan yi nasara ba.

A bangaren aikin gwamnati kuma, na fara a matsayin malamin makaranta a nan Jihar Kano daga baya kuma na koma Abuja a matsayin ma’aikacin gwamnati. A lokacin na kasance ina matsayin shugaban kananan hukumomi uku da suka hada da Gwagwalada da Abaji and Kwali. Daga baya kuma sai na zamo Darakta a Gwamnatin Tarayya. Bayan haka sai wani dalili ya dawo da ni Kano a mastayin Kwamishinan Ayyuka da Gidaje, da Sufuri na Jihar Kano. Na yi aiki a zamanin gwamnonin mulkin soja uku a Jihar Kano.

Kwatsam, sai na kara komawa fagen siyasa bayan an sake dawo da siyasar dimokuradiyya wanda hakan ya sa na zamo Mataimakin Gwamna har zuwa matakin da na tsinci kaina a yanzu. Na rike matsayin kwamishina tsawon shekara shida. Kuma  na rike matsayin Mataimakin Gwamna tsawon shekara takwas. Ga shi kuma yanzu ina matsayin Gwamna tsawon shekara shida zan shiga ta bakwai. Zan iya cewa na yi gwagwarmaya a fagen siyasa da kuma aikin gwamnati.

Lura da irin munafuncin da ke cikin siyasa da aikin gwamnati, ta yaya ka tserar da kanka har zuwa matakin da kake yanzu ?

Wato ba zan iya kiran hakan da munafunci ba, sai dai in ce kalubale wanda shi ya kamata mu rika sauyawa zuwa damammaki. Na dade ina fadin haka. Da farko dai ita siyasa wata dama ce da za a hidimta wa al’umma, musamman a tsarin dimokuradiyya da muke ciki.

Ita siyasa magana ce ta mu’amala a tsakanin al’umma, batu ne na sanin ina aka dosa. Magana ce ta samar da tsari da kuma samar da kudirin da ake so a cim ma.

Duk kokarin da ake domin rage cinkoso a gidajen yari, alamu sun nuna har yanzu gwamnoni suna kin sa hannu a kan hukucin kisa da kotuna suke yankewa, me ya sa hakan?

Shi batun sanya hannu a kan hukuncin kisa ga wadanda aka yanke musu hukuncin yana da alaka da tsare-tsaren doka da shari’a. Zan iya tuna lokacin da tsohon Gwamnan Jihar Edo ya sanya  hannu a kan hukunci kisa wanda doka ta umarta, sai bayan an kashe mutumin aka gano cewa bai kamata a kashe shi ba saboda an yi kuskure a shari’ar da kuma hukuncin da aka yanken. Tun bayan faruwar lamarin, gwamnoni suke fargabar rattaba hannu a hukuncin kisa. Amma duk da haka, lokaci-lokaci muna rattabawa.

Tabbas muna ganin ya kamata a yi duba na tsanaki domin ganin cewa an yi wani tanadi wanda zai  magance aukuwar kuskuren kashe wadanda bai kamata a kashe su ba. Duk wanda aka kashe ba za a dawo masa da rayuwarsa ba. Ina ganin wannan shi ne fargabar da mutane suke yi.

Kana ganin cewa gwamnoni kamar ba su da kwarin gwiwa a kan tanadin shari’a ke nan?

Wadansu daga cikin wadanda aka yanke wa hukuncin sun daukaka kara, kuma hakan yana daukar shekaru da yawa kafin a saurara. Wani lokacin ko ka rattaba hannu sai ka gano cewa tsarin daukaka karar bai gama kammala ba. Ina tunanin wannan lamari ne da ya kamata a ce an yi wa duba na tsanaki a bisa kundin tsarin mulkin kasar nan.

Amma me ya sa ’yan siyasa ba sa fargaba idan aka zo batun abin da zai amfane su, kamar canja jam’iyya?

Kana canja batun da muke yanzu. Kana maganar jam’iyun siyasa wadanda wasu kafafe ne da suke ba da damar gwagwarmaya a siyasance. Kana maganar siyasar hamayya, kana maganar dimokaradiyyar cikin gida, kana kuma maganar rikicin da ke aukuwa a tsarin dimokaradiyya a kasashe masu bunkasa kamar Najeriya.

Idan za ka iya tunawa, a 1999 lokacin da mulkin dimokuradiyya a Najeriya ya dawo, ba za ka iya canja jam’iyyar da kake ba, ba tare da ka ajiye mukamin da kake rike da shi wanda aka zabe ka ba. Amma saboda matsalolin da ake fuskanta a cikin tsarin dimokuradiyyar, wasu jam’iyun siyasar ba su iya magance hakan ba.

A matakin shugabancin kasa, ana zabar mutum ne ta dalilin jam’iyyar  siyasar da ya fito da kuma cancantarsa. Yanzu idan har za ka ajiye mukaminka saboda za ka canja jam’iyya hakan yana nufin ita jam’iyyar ce ke da alhakin zabenka. Saboda haka idan har za a yi la’akari da lamarin siyasar jami’iyya hakan yana nufin ke nan mutum ba ya da duk cancantar da yake da ita saboda kawai ya canja jami’yya.

Ina tunanin wannan lamari ne da yake da alaka da dimokuradiyya,  muna kokarin gyarawa kuma har yanzu muna kokarin fahimatr matakin lamarin wanda zai iya kai mu zuwa ga akidar siyasa. Saboda haka yana da matukar wahala a ce an ajiye batun canja jam’iyya zuwa wata jam’iyya.

Shin ya kamata a samu akida a lamarin siyasa?

Tabbas, ya kamata a ce akwai akida. Kuma hakan yana faruwa. Ba laifi ba ne idan  kundin tsarin mulki ko gwamnati ta sahale samar da akidun siyasa. Lamari ne da yake karfafa kuma idan lokaci ya yi zai tabbata. Yanzu siyasa tana sauya salo kuma mutane sun kara wayewa, hatta masu jefa kuri’a su ma sun samu wayewa sosai. Ina da yakinin za a kai ga lokacin da mutane za su fara tambayar me ya sa kana wannan jam’iyya ka canja zuwa wancan? Me ya jawo ra’ayinka?

Amma mutane da yawa sun kasa bambance tsakanin APC da PDP, saboda cewa duka ’yan siyasarsu ne suke ta canja sheka daga nan zuwa can domin su lashe zabe…

Tabbas wannan magana haka take. Kamar yadda na gaya maka, muna cikin tsarin ci gaba ne, nan gaba kadan mutane za su gaji da wannan sauyin jam’iyya da ake yi. Zai zamo mutane sun fara tsayawa a kan tsarin kasancewa a jam’iyya daya kamar yadda ake yi a kasar Amurka.

Muna kwaikwayon tsarin mulkinsu, amma duk da haka mutane ba su fasa canja jami’yya ba, daga wannan zuwa wancan. Amma ina ba ka tabbacin nan gaba hakan zai iya zama kalubale babba.

Kana nufin za ku ruguza kwamitin da Buni ke jagoranta, ku sake wani zaben, kuma ba tare da kun sake maimaita irin abubuwan da suka faru ba kamar zaben shugabannin mazaba da sauransu?

Wato shi wannan mulki ba dauwamamme ba ne, kamar yadda sunan ya tabbatar, za su kasance a wannan matsayin zuwa dan wani lokaci kadan kawai kafin lauyoyinmu su kammala shirin da ya dace a bisa kundin tsarin mulkin jam’iyya da kuma kundin tsarin mulkin Najeriya. Idan muka samu tabbacin cewa wannan abu da muka yi babu  kuskure a ciki a bisa doka, to za mu ci gaba da haka.

Akwai jita-jitar cewa kana da dan takarar da kake son tsayarwa wanda zai gaje ka don zama Gwamnan Jihar Kano bayan ka sauka, shin akwai wanda kake so ka tsayar ?

Lamarin ba nan kusa ba ne, kuma labarin da kuka ji game da hakan ba gaskiya ba ne. Wannan kalaman batanci ne, kuma al’ummar Jihar Kano sun sani cewa babu wanda muka tsayar a matsayin dan takarar Gwamnan Jihar Kano, ko dan takarar Sanata ko kuma kowane irin matsayi. Hankalinmu ya fi karkata zuwa ga tsarin mulki har zuwa lokacin da hukumar zabe za ta fitar da jawadalin zaben .

Saboda haka ina mai ba ku tabbacin cewa duk ’yan takarar da suke son tsayawa suna da nagarta, kuma sun cancanta. Idan lokaci ya yi, hakkinmu ne mu tattauna mu yi abin da ya dace, domin mu yi zaben kamar yadda tsari da dokar jam’iyyarmu suka tanada bisa kundin tsarin mulkin Najeriya.