✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ban umarci sojoji su kashe ‘yan kabilar Igbo a Ribas ba – Wike

Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike ya musanta zargin da ake masa cewa ya umarci sojoji su kashe ‘yan kabilar Igbo

Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike ya musanta zargin da ake masa cewa ya umarci sojoji su kashe ‘yan kabilar Igbo a karamar hukumar Oyigbo ta jihar.

Ya bayyana zargin a matsayin karyar ‘yan siyasa, yana mai cewa ya sanya dokar ta baci ne domin dawo da zaman lafiya bayan ‘yan haramtacciyar kungiyar nan mai fafutukar kafa kasar Biafra ta IPOB sun yi ta’asa a yankin.

Gwamnan wanda ya bayyana hakan yayin wani jawabi da ya yi wa al’ummar jihar kai tsaye ta kafar talabijin ranar Litinin ya kuma ce ‘yan kungiyar sun hallaka jami’an tsaro 10 tare da kona ofishin ‘yan sanda a yankin.

A cewarsa, zargin kisan ‘yan kabilar Igbon da ake yi wa sojojin wani yunkuri ne na kautar da hankulan mutane daga ta’asar da kungiyar ke yi a yankin wanda ke da iyaka da jihar Abiya.

Wike ya ce, “Na san wannan ba shine karon farko da IPOB ke amfani da yankin wajen yin haramtattun ayyukansu ba, jami’an tsaro na da masaniya a kan haka. Yanzu haka ma sun sake canza salo.

“Sun hallaka jami’an ‘yan sanda guda hudu, sun kuma lalata dukkan ofisoshinsu tare da wani ginin kotu. Shin wanne laifin muka aikata musu a matsayinmu na jiha?

“Na sanya dokar hana fita ne don dawo da zaman lafiya a jihar, kuma na haramta ayyukan IPOB a kowanne yanki na jihar.

“Kada a manta, hatta Gwamnatin Tarayya ta ayyana kungiyar a matsayin ta ‘yan ta’adda. Amma ba dukkan ‘yan kabilar Igbo ne suka yi amanna da ayyukan IPOB ba.

“Saboda haka ba gaskiya bane cewa na umarci sojoji su hallaka ‘yan kabilar a Oyigbo. Yaushe ma ni na zama abokin sojojin? Ina kuma sauran ‘yan kabilar dake zaune a wasu sassa na jihar? Su kuma wa ya kai musu hari?,” inji Wike.

Gwamnan ya kuma koka kan yadda ya ce IPOB ta canza sunan wata karamar hukuma a jihar tare da kafa tutarta a wata makarantar gwamnati a garin Komkom dake jihar.