Ban yarda da addini ba —Wizkid | Aminiya

Ban yarda da addini ba —Wizkid

Mawaki Wizkid
Mawaki Wizkid
    Ishaq Isma’il Musa

Fitaccen mawakin Kudancin Najeriya mai salon kidan Afrobeats, Ayo Balogun wanda aka fi sani da Wizkid, ya bayyana cewa bai gaskata addini ba.

Wizkid ya bayyana hakan ne cikin wani sako da ya wallafa a bayan nan a shafinsa na Snapchat.

A cewarsa, “Ba na tashi daga bacci da wani bacin rai ko damuwa a raina.

“Ba na tashi na tsinci kaina cikin talauci ko tsiya a rayuwa ko a lafiyata da kuma cikin ruhi.

“Ba na tashi da wata kiyayya ko bakin ciki a zuciyata.

“Kada ku bata rayuwarku a kan wani lamari na dan lokaci. Ku yi rayuwa domin kuwa yawan shekaru ba sa maunin dabarar kowane mutum ba.

“Akwai mutane da dama da na sani wadanda sun girma sun tara shekaru amma wawaye ne kuma ba su da wata dabara sannan kuma ni ban yarda da addini ba.”

A watan Nuwambar bara ne Wizkid ya lashe kyaututtuka a bikin bayar da kyautar mawaka ta AFRIMA 2021.

Mawakin dai ya lashe kyautar mawakin shekara, wakar shekara da kuma wakar hadin gwiwa ma fi shahara a bikin da aka gudanar a birnin Legas.