✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ban yi wa sassan jikin Hanifa gunduwa-gunduwa ba —Abdulmalik Tanko

Babu wanda ya dauki wuka ko wani abu ya illata jikinta.

Shugaban Makarantar Noble Kids da ke unguwar ’yan Kaba kwanar Dakata a birnin Kano, Abdulmalik Tanko wanda ake tuhuma da laifin yin garkuwa da kuma kashe Hanifa Abubakar, ya ce ba gaskiya ba ne rahotannin da ake yayatawa cewa an yi gunduwa-gunduwa da jikinta bayan ta mutu kafin aka binne ta.

Abdulmalik ya shaida wa Muryar Amurka hakan ne yayin da yake amsa tambayoyin wakilinta, inda ya yi karin haske kan wasu daga ciki al’amuran da suka danganci rayuwar Hanifa bayan shigarta hannunsa har zuwa lokacin da ya kashe ta kuma ya binne gawarta.

Ya bayyana cewa, an sa Hanifa a cikin buhu ne wanda ba shi da girma sosai duk da cewa yana da fadi da ya zama dole kafarta ta tankware.

A cikin bidiyon da VOA ya nada, Abdulmalik ya ce, “An sa ta ne a cikin buhu, kuma da yake ita karamar yarinya ce buhun ya dan yi mata kadan duk da cewa yana da fadi, sai aka dan lankwasa gwiwarta da kafarta yadda dukan jikinta zai shiga buhun amma babu wanda ya dauki wuka ko wani abu ya illata jikinta.”

A cewarsa, tankware kafafunta kafin sa ta buhun da aka binne ta a ciki, ya sa lokacin da aka tono ta, aka ga kamar an karya gababuwanta, amma a zahiri ba wanda ya daddatsa ta ko wani abu makamancin haka.

Aminiya ta ruwaito cewa, a kokarin daukar matakin ladabtarwa, Abdulmalik ya bayyana a gaban kotu karon farko a ranar Litinin.

Abdulmalik Tanko tare da sauran mutum biyu da ake zargin hannunsu a kisan Hanifa

Abdulmalik ya bayyana gaban kotun ne tare da mutane biyu, Hashimu Ishiyaku, da Fatima Jibrin Musa da ake zargi suna da hannu a garkuwa da kuma mutuwar Hanifa.

Bayan sauraron karar, Lauyan gwamnati kuma Mai shari’ah Muhammad Lawan ya dage sauraron karar zuwa ranar 2 ga watan Fabrairun wannan shekara domin ba lauyoyin gwamnati da za su kare Abdulmalik damar gudanar da nasu binciken.

Kotun tana tuhumar mutanen uku da laifuka da suka hada da hada baki, garkuwa, boyewa da kuma ajiye yarinyar da suka yi garkuwa da ita a wuri daya, da kuma kisan kai, laifukan da suka amsa aikatawa.