2023: Bangaren Wike ya fice daga kwamitin yakin neman zaben Atiku | Aminiya

2023: Bangaren Wike ya fice daga kwamitin yakin neman zaben Atiku

  Victor Edozie, Fatakwal da Sagir Kano Saleh

Bangaren da ke goyon bayan Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike, ya janye daga kwamitin yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar a zaben 2023.

A safiyar Laraba, suka sanar da ficewarsu daga kwamitin yakin neman zaben Atiku bayan wani zama da suka yi a gidan Wike da ke Fatakwal.

Da yake sanar da mastayin nasu bayan taron, Cif Olabode Goerge ya ce babu abin da zai sa su yi kowane irin aiki a kwamitin, face Shugaban Jam’iyyar PDP na Kasa, Iyorchia Ayu, ya sauka daga mukaminsa.

Mahalarta taron bangaren sun hada da:

 • Gwamnan Jihar Oyo  Seyi Makinde
 • Tsohon Gwamnan Jihar India, Olusegun Mimiko
 • Tsohon Gwamnan Jihar Kuros Riba, Donald Duke
 • Tsohon Gwamnan Jihar Ekiti, Ayo Fayose
 • Tsohon Gwamnan Jihar Filato, Jona Jang
 • Tsohon Ministan Shari’a Mohammed Adoki
 • Sanata Olabode George
 • Tsohon Minista Farfesa Jerry Gana
 • Dan takarar Gwamnan Jihar Katsina, Sanata Lado Danmarke
 • Tsohon Mataimakin Shugaban Jam’iyyar PDP na Kasa, Sanata Suleiman Nazif
 • Chibudom Nwuche
 • Nnenna Ukeje.