✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bangarorin da ke rikici a Libya sun tsagaita wuta

Manyan bangarorin da ba sa ga miciji a kasar Libya sun kulla yarjejeniyar tsagaita wuta ta dindindin ranar Juma’a bayan shafe kwana biyar suna tattaunawa.…

Manyan bangarorin da ba sa ga miciji a kasar Libya sun kulla yarjejeniyar tsagaita wuta ta dindindin ranar Juma’a bayan shafe kwana biyar suna tattaunawa.

Ana ganin rattaba hannu a kan jarjejeniyar wacce ta gudana a Majalisar Dinkin Duniya (MDD) a matsayin wani mataki mai cike da tarihi wajen magance rikicin kasar.

Wakiliyar MDD a Libya, Stephanie William ta bayyana ranar kulla yarjejeniyar a matsayin wata muhimmiya ga mutanen kasar.

Ta ce, “Da misalin karfe 11:15 na safe a agogon GMT, yau (Juma’a) a ofishin MDD da ke birnin Geneva, wakilan bangarorin Libya sun rattaba hannu a wata cikakkiyar yarjejeniya a duk fadin kasar kuma ta dindindin ba tare da wani bata lokaci ba.

“MDD ce ta jagoranci yarjejeniyar, mu kuma mun rattaba hannu a kanta a matsayin shaidu”, inji Misis Stephanie yayin wani taron ’yan jarida a Geneva.

Libya ta shafe kusan shekara 10 tana fama da rikici tun bayan hambarar da gwamnatin Shugaban Moammar Ghadhafi a wani bore da Kungiyar Tsaro ta NATO ta mara wa baya.

Tun a lokacin, kungiyoyi masu dauke da makamai ke cin karensu ba babbaka tsakanin muhimman bangarorin gwamnati da na ’yan tawaye.

To sai dai an samu kwarin gwiwar samun sassauci bayan da bangarorin a radin kansu suka amince za su tsagaita wuta, duk da cewa har yanzu suna zargin juna da goyon bayan ta’addanci.

Tattaunawar ta MDD ta kunshi mutane biyar-biyar daga kowanne bangare kafin a cimma matsayar.