✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bankin Duniya zai ba Afirka ta Kudu rancen $474m don sayo rigakafin COVID-19

Kasar dai ita ce wacce cutar ta fi yi wa illa a nahiyar Afirka

Bankin Duniya ya amince da ba kasar Afirka ta Kudu rancen Dalar Amurka miliyan 474.4 don ta sayo allurar rigakafin COVID-19.

Asusun Gwamnatin Tarayyar kasar da Babban Bankinta ne suka tabbatar da amincewar a cikin wata sanarwa a ranar Litinin.

Kasar dai ita ce ta fi kowacce a nahiyar Afirka yawan mutanen da suka kamu ko suka mutu sanadiyyar cutar.

Akalla mutum miliyan 3.9 ne aka tabbatar sun kamu da ita, yayin da sama da 101,000 kuma suka mutu sanadiyyarta.

Da farko dai kasar ta yi fama da matsaloli a yunkurinta na samar da rigakafin cutar ga mutanenta, amma yanzu bisa ga dukkan alamu matsalar ta tasam ma zuwa karshe.

“Wannan rancen zai taimaka matuka wajen sayo rigakafi miliyan 47, wanda Gwamnatin Afirka ta Kudu za ta yi,” kamar yadda sanarwar ta tabbatar.

A cewar mai rikon mukamin Shugaban Asusun kasar, Ismail Momoniat, bashin yana daya daga cikin hanyoyin da kasar ke bi wajen rage yawan kudaden da take kashewa a yaki da cutar.

Ya zuwa ranar Litinin dai, fiye da rabin baligan mutanen kasar su kimanin miliyan 40 ne suka karbi rigakafin COVID-19 akalla sau daya.