✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bankuna za su ci gaba da karbar tsofaffin kudi bayan cikar wa’adin CBN – Emefiele

Emefiele ya ce bankuna za su ci gaba da karbar tsofaffin kudi bayan wa'adin CBN ya cika

Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele ya ce bankunan kasuwanci za su ci gaba da karbar tsofaffin kudade bayan cikar wa’adin da CBN ya bayar na 10 ga watan Fabrairu.

Emefiele ya bayyana haka ne lokacin da ya bayyana a gaban kwamitin Majalisar Wakilai, a ranar Talata.

Sai dai kuma ya bayyana rashin dadinsa kan yadda wasu ke yi wa tsarin sauya tsofaffin kudaden zagon kasa a bankuna, duk da umarnin da CBN ya bayar.

Ya ce CBN ya aike karin jami’an hukumomin hana cin hanci da rashawa bankuna don taimaka musu wajen dakile wadanda suke yi wa shirin zagon kasa.

Ya ce tsarin takaita kudade na da matukar tasiri wajen hana hauhauwar farashin kayayyaki da kuma bunkasa tattalin arzikin kasa.

Kazalika, ya ce biyan kudaden fansa da mutane ke yi ga ‘yan bindiga na fuskantar tsaiko saboda a yanzu yana da wahala mutum ya dauki tsabar kudi ya fita da su.

Sai dai ya ce yana da masaniyar cewar wasu ‘yan Najeriya na iya fuskantar matsaloli game da tsarin, amma a cewarsa a sannu komai zai daidaita.

Har wa yau, ya ce babban bankin ya tura ma’aikatan na musamman guda 30,000 yankunan karkara da ka iya fuskantar wahalhalu game da sauya tsofaffin kudadensu.

Wannan dai na zuwa ne bayan karin kwanaki 10 da CBN ya yi na cikar wa’adin daina karbar tsofaffin kudi a fadin tarayyar kasar nan.