✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Bara kaskanci ne gare mu nakasassu’

Wani matashi mai yi wa kasa hidima da ke da nakasa a hannuwansa biyu, Imran Muhammad Musa, ya ce barar da wadansu nakasassu ke yi…

Wani matashi mai yi wa kasa hidima da ke da nakasa a hannuwansa biyu, Imran Muhammad Musa, ya ce barar da wadansu nakasassu ke yi na kawo musu kaskanci da wulakanci.

Imran wanda ya kammala karatun digirinsa a Bangaren Lissafi a Jami’ar Bayero da ke Kano, ya ce bara aba ce da ba ta kamata Musulmi ya mayar da ita sana’a ba.

Imran wanda ya ce an haife shi da nakasa a hannuwa ya ce ilimi shi ne mafita ga nakasassu don haka ya yi kiran su nemi ilimi maimakon yawon barace-barace.

“Bara ba ta dace da masu matsalar nakasa ba ko kadan, ba wai don kana da nakasa shi zai sa ka je kana yin bara ba domin kuwa bara kaskanci ne da wulakanci.

“Masu yin barar nan suna fuskantar wulakanci iri-iri kafin su samu sadaka wanda abin da ya dace da su shi ne neman ilimi don ko masu lafiyar ma da ilimi suke takama ballanatana masu nakasa.

“Idan kuma ba karatu suke son yi ba, to kamata ya yi su kama wata sana’a wacce za su dogara da ita”, inji shi.

Ya yi kira ga gwamnati ta rika taimaka wa masu nakasassu a harkar karatunsu da kuma samar musu da ayyukan yi.

“Ya kamata gwamnati ta saukaka harkar koyo ga masu matsalar nakasa, lura da cewa suna da lalura —bai kamata a dora musu wasu abubuwa kamar yadda za a yi wa masu lafiya ba.

“Haka kuma wajen samun aikin yi ya kamata gwamnati ta rika sanya su a farko-farko idan ta tashi dibar ma’aikata.

“Ya kamata a ce da sun kammala karatu suna da aikin da za su yi a kasa amma ba sai sun gama ba su rika yawon neman aiki kamar sauran masu lafiya ba”, inji shi.