✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Barayin waya sun yi wa alaramma yankan rago

Wasu masu kwacen waya sun yi wa wani masanin Al-kur’ani yankan rago a unguwar Dan Rimi layin Malama mai Dalla-dalla a karamar Hukumar Ungogo, Jihar…

Wasu masu kwacen waya sun yi wa wani masanin Al-kur’ani yankan rago a unguwar Dan Rimi layin Malama mai Dalla-dalla a karamar Hukumar Ungogo, Jihar Kano.

Masu kwacen sun yanka Alaramma Shu’iabu Bichi mai shekara 34 ne bayan sun far masa da tsakar ranar Juma’a da dare dakinsa.

Kafin rasuwarsa mamanin yana sana’ar tuka babur mai kafa uku ne.

Mazauna unguwar sun ce masu kwancen sun fahimci malamin bai rufe kofarsa ba lokacin da ya kwanta barci, sai suka yi amfani da damar suka afka masa.

Wani mazaunin unguwar, Jabir Abubakar Danrimi, ya ce ’yan ta’addar da suka shiga dakin mamacin sun yi ta sarar sa bayan sun kwace masa waya da sauran kayansa.

“Alaranma Shu’aibu Bichi mutumin kirki ne shekararmu 15 tare da shi, koyaushe cikin mu’amula mai kyau yake da mutane, ni dai ban taba  ganin fadarsa ba”, inji shi.

Shehu Muhammad, ya ce kashe malamin ya tayar mus da hankali, sai da ya gagara fitowa saboda alhinin rasuwar.

Mutanen Dan Rimi da suka ce an sha yin irin haka a unguwar, sannan suka yi roko ga gwamnati da hukumomin tsaro su kawo musu dauki don magance ayyukan ta’addanci a unguwar tasu.

Tuni Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Kano ta ba wa ’yan uwan mamacin gawarsa aka yi jana’izarsa kamar yadda Musulunci ya tanada.

Matsalar kwacen waya a Kano:

A kwanakin baya an sha yin artabu da masu kwacen waya a birnin Kano inda Shataletalen Kofar Dan Agundi da katangar Kwalejin Rumfa suka zama matattarar masu yin kwacen waya.

Bata-garin kan yi wa mutanen da ke kan babura kwacen waya wani lokaci har da daba musu wuka.

Matsalar kwacen waya na tayar wa mutane hankali sosai ta yadda suke rasa sukunin ciro waya a kan hanya.

Rundunar ’yan sanda mai yaki da ayyukan daba a Jihar Kano ta kame barayin waya da dama a yankin na Dan Agundi zuwa Sabuwar Kofa.