✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Barazanar shan miyagun kwayoyi ta fi ta ta’addanci a Najeriya – Buhari

“Na sha ganin hotunan kakanni da iyaye da ’ya’yansu suna shan kwaya” inji shi.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ce barazanar da sha da fataucin miyagun kwayoyi ke yi ga Najeriya ta fi ta ayyukan ta’addanci da garkuwa da mutane.

Ya bayyana hakan ne ranar Asabar a Abuja yayin kaddamar da yaki da miyagun kwayoyi da aka yi wa lakabi da WADA wanda Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi (NDLEA) ta shirya domin bikin ranar yaki da kwayoyin ta Majalisar Dinkin Duniya.

A cewar Shugaban, “Ina so in shaida muku cewa wannan yakin yafi wahala fiye da ayyukan ta’addancin da muke fama da shi a yankin Arewa maso Gabas da na ’yan bindiga a Arewa maso Yamma wanda yanzu haka ya fantsama zuwa sauran shiyyoyin kasar nan saboda yaki ne da ke barazana ga al’ummomi har hawa uku.

“Na sha ganin hotunan kakanni da iyaye da kuma ’ya’yansu duk suna ta’ammali da miyagu kwayoyi,” inji shi.

Shugaban wanda ya sami wakilcin Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha ya yi kira ga NDLEA da ta kara azama wajen fatattakar miyagun da ke amfani da dazukan Kudancin kasar nan wajen noman Tabar Wiwi.

“Yaki da shan miyagun kwayoyi yaki ne da ke bukatar gudunmawar kowa da kowa. Saboda haka nake kaddamar da wannan shirin na WADA a madadin al’ummar Najeriya, ba wai a matsayin take kawai ba, amma a matsayin wani shirin kawo sauyi a kasar.”

Buhari ya kuma yi kira ga iyalai, makarantu, kungiyoyin fararen hula da na masu sana’o’i, kungiyoyin addini, malamai da shugabannin al’umma da sauran daidaikun mutane su yi aiki tare don magance matsalar tun daga tushe.

Shi kuwa a nasa jawabin, shugaban hukumar NDLEA, Birgediya Janar Buba Marwa mai ritaya ya ce kimar kwayoyin da hukumar ta kwace a watanni biyar din day a yi a hukumar yah aura Naira biliyan 90.

Ya kuma ce sun sami nasarar cafke gaggan masu safarar kwayoyin har 2,180, ciki har da wasu rikakkun dillalai biyar da suka gagari Kundila, yayin da suka gurfanar da sama 2,100, sai kuma 500 da aka daure.

Buba Marwa ya kuma ce alkaluma sun nuna cewa Najeriya ce kasar da ta fi yawan masu shan Tabar Wiwi a duk fadin duniya, lamarin da ya ce yana taimakawa matuka wajen kara tabarbarewar al’amuran tsaro.

Taron ya kuma sami halartar Shugaban Majalisar Dattijai, Sanata Ahmed Lawan wanda Shugaban Kwamitin yaki da Miyagun Kwayoyi na Majlisar, Sanata Ezekiel Dimka ya wakilta, da Kakakin Majalisar Wakilai, Femi Gbajabiamila, wanda Hon. Francis Agbo ya wakilta.

Sauran manyan bakin sun hada da wakilin Babban Magatakardar Majalisar Dinkin Duniya Antoni Guterres da wakilin Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar da dai sauransu.