✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Barazanar tsaro ta janyo rufe makarantun FGC a Abuja

Gwamnatin Tarayya ta dauki matakin ne saboda karuwar barazanar tsaro da makarantun FGC ke fuskanta a Abuja

Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya ta bada umarnin rufe dukkanin makarantun sakandaren Gwamnatin Tarayya da ke Birnin Tarayya sakamakon barazanar tsaro da makarantun hadaka ke fuskanta a Abujan.

Daraktan Yada Labarai na Ma’aikatar, Mista Ben Goong ne ya tabbatar wa manema labarai hakan a ranar Litinin, inda ya ce tuni ma’aikatar ta bada umarnin kwashe dalibai daga makarantun, domin tsira da rayukansu.

Daraktan ya ce umarnin ya biyo bayan karuwar tabarbarewar sha’anin tsaro a birnin da ta zamo barazana ga makarantun, shi ya sanya suka dauki wannan mataki na gaggawa.

Idan za a iya tunawa dai Gwamnatin Tarayya ta  bukaci wasu daga cikin makarantun da su rufe a ranar 20 ga watan Yuli, yayin da wasu kuma za su rufe a ranar 26 ga watan.

To sai dai Makarantar Sakandaren Gwamnatin Tarayya da ke Kwali ta bukaci iyaye da su kwashi ’ya’yan nasu a ranar Litinin, sakamakon wannan umarni na ma’aikatar ilimin.

Aminiya ta kawo rahoton yadda  dalibai na tserewa gida bayan ’yan bindiga sun kai hari a kusa da Makarantar Sakandaren Gwamnatin Tarayya (FGC) da ke Kwali a Abuja.

Iyayen daliban makarantar sun yi ta sammakon zuwa kwashe ’ya’yansu ne bayan farmaki da aka kai a kauyen Sheda da ke daura da makarantar a kan babbar hanyar Abuja zuwa Lakwaja.

Waki mu ya ziyarci makarantar a safiyar Litinin, inda ya yi kicibus da wasu iyaye da suka je suka dauki ’ya’yansu.

Mahaifiyar wata daliba ta ce ta yiwo takakkiya ne daga Legas domin ta kwashe bayan hukumar makarantar ta sanar da ita ta wayar tarho.

Ta ce bayan samun kiran da Al’adar ranar Lahadi ne ta biyo motar dare zuwa Abuja domin dauka ’ya’yanta mata biyu kamar yadda hukumar makarantar ta bukaci iyayen dalibai.

“Da misalin karfe 4 ’yata ta kira ni ta wayar mai kula da ita cewa ana bukatar iyaye su gaggauta zuwa su dauki ’ya’yansu saboda barazanar harin ’yan bindiga a makarantar,” inji ta.

Ta bayyana takaici bisa yadda lamarin ya kawo tsaiko ga jarabawar da ’ya’yan nata, amma ta ce Gara hakan da a yi badi ba rai.