✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Barcelona ba ta cire rai kan batun Neymar da Griezmann ba – Bartomeu

A shekaranjiya Laraba ce Shugaban Kulob din FC Barcelona da ke Sifen, Josep Maria Bartomeu ya fada wa manema labarai cewa har yanzu kulob din…

A shekaranjiya Laraba ce Shugaban Kulob din FC Barcelona da ke Sifen, Josep Maria Bartomeu ya fada wa manema labarai cewa har yanzu kulob din bai cire rai wajen sayo dan kwallon Paris Saint Germain (PSG) na Faransa Neymar Jnr da kuma Antonio Griezmann dan kwallon Atletidco Madrid da ke Sifen ba.

Magoya bayan kulob din sun shiga rudu saboda ganin an kusa fara kakar wasa ta bana kuma babu wani takamaiman bayani game da sayo wadannan zaratan ’yan kwallo.

Neymar wanda ya canja sheka daga Barcelona zuwa PSG kimanin shekara uku da suka wuce yana son sake komawa kulob din ne kafin a fara kakar wasa ta bana al’amarin da ya sa yanzu haka ya ki yin atisaye da kulob din PSG a matsayin yajin aiki don a sayar da shi ga FC Barcelona.

Rahoton da ke fitowa daga Sifen ya nuna Antonio Griezmann dan kwallon gaba a Atletico Madrid shi ma ya ki halartar wasannin atisayen da kulob din ya fara a kokarin tunkarar kakar wasa ta bana saboda hankalinsa ya koma kan kulob din FC Barcelona.

Sai dai  zuwa shekaranjiya Laraba babu wata kwakkwarar shaida da ta nuna an kusa kulla cinikin ’yan kwallon wanda hakan ya jefa dubban magoya bayan Barcelona cikin rudani.