✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Barcelona ta bayyana makomar Koeman

An jima ana rade-raden Barcelona na iya raba hanya da Koeman.

Rahotanni sun bayyana cewar, tuni shugaban kungiyar kwallon kafa ta Barcelona, Joan Laporta, ya sanar da kocin kungiyar cewar yana neman sabon mai horarwa da zai karbi kungiyar.

Laporta ya sanar a ranar Talata cewa Barcelona za ta nemi sabon koci nan da sati biyu masu zuwa.

Tuni gidan talabijin na TV3 da ke kasar Spain ya fara bayyana wadanda ake tunanin za su maye gurbin Ronald Koeman.

Sai dai a ranar Laraba wakilin kocin, Rob Jansen, ya sanar da cewa yana da yakinin Koeman zai iya ci gaba a matsayin kocin Barcelona.

Ya zuwa yanzu dai babu wata sanarwa ta musamman daga bangaren Barcelona ko Ronald Koeman kan tafiyar kocin.