✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Barcelona ta ci ribar Fam miliyan 86

Kungiyar kuma kuma tana sa ran samun ribar Fam miliyan 240 a 2023

Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta sanar da cin ribar kasuwancin ta Fam miliyan 86 (kimanin Naira biliyan 52) a shekarar da ta gabata, kuma tana sa ran samun ribar Fam miliyan 240 a shekara mai zuwa.

A bara kungiyar ta kasa daukar sababbin ’yan kwallo, saboda bin dokar kashe kudi daidai da samu ta Hukumar La Liga.

Barcelona ta fada matsin tattalin arziki a bara, inda ta yi asarar Fam miliyan 422 da ta kai Lionel Messi ya bar Camp Nou zuwa Paris St Germain.

Duk da haka kungiyar ta kare a mataki na biyu a gasar La Liga, amma ba ta taka rawar gani ba a sauran wasannnin da ta fafata a kakar da ta wuce.

Daga baya ne kungiyar ta dauki matakan da suka dace don mayar da ita cikin fitattu a fannin taka leda a duniya.

Barcelona ta ce ta samu kudin shiga da ya kai Fam miliyan 890 a kakar 2021/22.

Kungiyar ta hadu da tsaiko kafin ta yi wa sababbin ’yan kwallon da ta dauka a bana rajista da suka hada da Robert Lewandowski da Raphinha.

Hakan ya biyo bayan da La Liga ta yi bincike don tabbatar da Barcelona na bin ka’idojin da aka gindaya a hukumance.

Hanyoyin da kungiyar ta bi don fita daga kangin da take ciki, sun hada da sayar da hannun jarin nuna wasanninta a talabijin a nan gaba da cefanar da mallakar gabatar da shirye-shiryen a Barca Studios.

A cikin watan Agusta ta sayar da karin kashi 24.5 cikin 100 na Barca Studios ga Orpheus kan Fam miliyan 84.6, hakan ne ya sa ta samu isassun kudin yin rajistar wasu ’yan wasan da ta dauka a kakar nan.

Barcelona tana mataki na biyu a teburin La Liga da maki 16, bayan wasa shida da fara a babbar gasar tamaula ta Spain ta bana da tazarar maki shida a tsakaninta da Real Madrid mai jan ragama.