✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Barcelona ta kammala cinikin daukar Lewandowski daga Bayern Munich

Barcelona ta dauko tauraron daga Alianz Arena shekara guda bayan tafiyar Lionel Messi

Barcelona ta tabbatar da kammala cinikin daukar Robert Lewandowski daga Bayern Munich.

Tabbatar da yarjejeniyar na zuwa ne a karshen kwan-gaba-kwan-baya da aka rika yi tun bayan mika tayin sayen dan wasan kafin kakar wasanni ta 2021-22 ta kare.

Barcelona ta dauko tauraron daga Alianz Arena shekara guda bayan tafiyar Lionel Messi.

Barcelona za ta biya farashin Yuro miliyan 45 (£38m/$45m) don kawo Lewandowski zuwa Catalunya, tare da karin Yuro miliyan 5 na wasu tsarabe-tsarabe da za a iya karawa idan aka cim ma wasu sharuddan.

Sanarwar da kulob din ya fitar ta ce: “FC Barcelona da Bayern Munich sun cimma yarjejeniya kan cinikin Robert Lewandowski, bisa sharadin tabbatar da koshin lafiyar dan wasan sannan ya rattaba hannu kan kwantiraginsa.”

Ana sa ran Lewandowski zai rattaba hannu kan kwantiragin farko na shekaru uku tare da zabin tsawaita shi da shekara guda, wanda ke nufin zai iya ci gaba da zama a Camp Nou har zuwa karshen kakar wasa ta 2025-26.

A shekarar 2014 ne Lewandowski ya koma Bayern Munich daga Borussia Dortmund bayan karewar kwantiraginsa.

Barcelona dai na fatan Lewandowski ya doka mata wasannin rangadin shiga sabuwar kaka da za ta doka a Amurka ranar 26 ga watan Yuli.