✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Barcelona ta maka PSG a kotu don dakile kulla yarjejeniya da Messi

Ana zargin PSG na shirin karya dokar ‘Financial Fair Play Rule’.

Barcelona ta shigar da kara kotu inda ta mika bukatar hana kungiyar Paris Saint-Germain kulla yarjejeniya da tsohon dan wasanta, Lionel Messi.

Jaridar wasanni ta Marca da ke Spain, ta ruwaito cewa lauyan Barcelona Juan Branco ne ya shigar da karar gaban Kotun Hukumar Gudanarwar Kungiyar Tarayyar Turai EU, da ke birnin Paris.

Hujjar da Barcelona ta gabatar cikin korafin nata shi ne yadda PSG ke shirin karya dokar da ke haramta wa kungiyoyi kashe kudade fiye da abinda suke samu da aka fi sani da ‘Financial Fair Play Rule’ a turance.

Juan Branco ya nemi kotun da ta yi la’akari da albashin manyan ’yan wasan da PSG ta saya a baya bayan nan da suka hada da Sergio Ramos, Wijnaldum, Achraf Hakimi, Gianluigi Donaruma, kari a kan albashin Marco Veratti, Neymar da Mbappe, ’yan wasa mafi ya tsada da take da su, baya ga Messi da ake sa ran yana tafe.

Tun a ranar 1 ga watan Yuli Messi ya kasance dan wasa mai zaman kansa bayan karewar kwantaraginsa, lamarin da ya sa PSG ba za ta bukaci biyan Barcelona ko da sisi ba kan kulla yarjejeniya da shi.