✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Barcelona ta sallami kocinta Quique Setién

Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta sallami mai horas da 'yan wasanta Quique Setién.

Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta sanar da sallamar mai horas da ‘yan wasanta Quique Setién.

Sallamar na zuwa ne kwana biyu bayan kungiyar Bayern Munich ta yi wa Barca ci 8-2 a Gasar Zakarun Turai.

Sanarwar da Barcelona ta fitar a Litinin 17 ga watan Agusta ta ce, sallamar kocin na daga cikin garambawul din da take yi wa kanta.

“Daga yanzu Quique Setién ba shi ba ne kocin kungiyar mafi tashe. Nan gaba za a sanar da sabon kocin, daga cikin sauye-sauyen da muke yi”, kamar yadda ta wallafa a shafinta.

Ta ce Kwamitn AMintattun Barca ta amince da shawarar sallamar Quique Setién, wanda ya fara horas da ‘yan wasanta a ranar 13 ga Janairu, 2020.

A tsawon zamansa na wata bakwai, Quique ya jagoranci kungiyar a wasanni 25.

A cikinsu wasannnin ya samu nasara a 16, ya yi kunnen doki hudu sannan yayi rashin nasara biyar.

Matakin da kungiyar ta dauka na zuwa ne kwana biyu bayan kungiyar Bayern Munich ta lallasa Barca da ci 8-2 a Gasar Zakarun Turai.