✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Barcelona ta sallami kocinta Ronald Koeman

Barcelona ta gaza jure irin koma bayan da take samu karkashin Koeman.

Shan kashi da Barcelona ta yi a hannun Rayo Vallecano ya yi sanadiyyar rasa aikin Ronald Koeman.

Barcelona ta gaza jure irin koma bayan da take samu karkashin kocin nata dan asalin kasar Netherlands.

Bayan yin rashin nasara a hannun Real Madrid a karshen mako, kungiyar ta sake yin rashin nasara a ranar Laraba, wanda hakan yasa mahukunta kungiyar ta Barcelona suka raba gari da Koeman.

An shafe watanni ana ta rade-radin Barcelona za ta sallami kocin, amma hakan ba ta samu sai bayan da ta sha kashi a filin wasa ma Vallecas.

Yanzu Barcelona za ta shiga zawarcin kocin da zai ci gaba da jan ragamar kungiyar.

Tsohon dan wasan kungiyar Xavi Hernandez, yana jan ragamar kungiyar Al Sadd da ke kasar Qatar.