Daily Trust Aminiya - Barcelona za ta maye gurbin Dembele da Sterling, Chelsea za

Haaland da Hakimi

Barcelona za ta maye gurbin Dembele da Sterling, Chelsea za ta yi zari wajen daukar Haaland da Hakimi

Barcelona ta kyallara idanunta kan dan wasan Manchester City na kasar Ingila, Raheem Sterling, mai shekara 26, wanda take ganin yana da cancantar maye gurbin dan wasanta na kasar Faransa, Ousmane Dembele muddin ya ki sabunta yarjejeniyarsa. (Sport Mole)

Tottenham ta fara tuntubar dan wasan Borussia Monchengladbach, Marcus Thuram, don ganin ko za ta samu nasarar daukarsa kafin a rufe kasuwar ’yan kwallo. (Daily Mail)

Rafa Benitez, tsohon dan wasan Liverpool da New Castle, ya shiga sahun wadanda ke takarar maye gurbin kocin Everton da ya koma Real Madrid, Carlo Ancelotti. (Telegraph)

Chelsea ta nuna sha’awar kulla yarjejeniya da dan wasan Inter Milan na kasar Morocco, Achraf Hakimi, dan wasan mai shekara 22 wanda kuma ya karbi tayi daga Paris Saint Germain. (Goal)

Arsenal ta bi sahun Manchester United, Liverpool da Tottenham wajen farautar dan wasan Brighton & Hove Albion, Ben white wanda aka sanya wa farashin fam miliyan hamsin. (Metro)

Mai tsaron ragar Manchester United na kasar Sifaniya, David de Gea, na fatar ci gaba da zama a United har zuwa bayan kaka. (Sportslens)

Mai kungiyar Chelsea, Roman Abramovich, ya shirya fitar da fam miliyan 154 domin daukar dan wasan Dortmund, Erling Haaland. (Chelsea News)

Dan wasan baya na Sifaniya, Sergio Ramos, na fatar soma tattaunawa da Real Madrid domin tsawaita kwantaraginsa da shekara guda. (Sportlens)

West Ham ta dauki dan wasan tsakiya na Chelsea mai shekara 19, Pierre Ekwah, a kan farashin da a bayyana ba (Football 365).

AS Roma ta gabatar da fam miliyan 17 domin daukar kyaftin din Torino, a yayin da sabon kocinta, Jose Mourinho, ya nuna sha’awa kan dan wasan. (Calciomercato)

Karin Labarai