✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Barci ya kwashe wasu matukan jirgin sama a sararin samaniya

Sun farka ne yayin da wata kararrawa ta jirgin da ke sarrafa kansa ta ankarar da su cewa sun wuce iyaka.

Barci ya dauke wasu matukan jirgin sama biyu mallakin kasar Habasha a yayin da yake tsaka da balaguro a sararin samaniya.

Jirgin kirar Boeing 737 mai dauke da fasinjoji 154, ya tashi ne daga birnin Khartoum na Kasar Sudan zuwa birnin Addis Ababa na Habasha a farkon makon nan.

Masu tukin su na sararin samaniya da nisan kafa 37,000 tsakaninsu da kasa, sai barci ya dauke su gabanin isowarsu filin jirgin saman Addis Ababa inda za su sauka.

Masu kula da tashi da kuma saukar jiragen sama a filin, sun yi ta kokarin ankarar da su cewa suna daf da wuce inda ya kamata su soma saukar da jirgin, amma masu tukin jirgin ba su farga ba.

Daga karshe dai matukan jirgin sun farga ne yayin da wata kararrawa ta jirgin da ke sarrafa kansa ta yi kara don ankarar da su, cewa sun wuce iyaka, sannan suka farka daga likimon da suka yi.

Kafofin watsa labarai sun ruwaito cewa, matukan sun samu damar sauko da jirgin a iyaka ta biyu ta inda ya kamata su saukar da jirgin bayan sun wuce iyaka ta farko.

Mutane da yawa ne suka rika tofa albarkacin bakinsu daga ban mamaki da takaici, zuwa tausayi da alhini, la’akari da yadda matuka jiragen sama na kamfanin ke wahalar jigila babu isasshen hutu a aikinsu.

Wannan dai na zuwa ne bayan faruwar makamancin wannan lamari kamar yadda kafar watsa labarai da ABC 7 ta ruwaito yadda wasu matukan jirgi biyu suka bige da barci a watan Afrilu bayan tasowa da daga birnin New York na Amurka zuwa birnin Rome na Italiy dauke da fasinjoji kusan 250.

Rahotanni na cewa, wahalhalun jigilar jirage da ke janyo wa matuka jirgin sama gajiya na daya daga cikin kalubalen da ake fuskanta a harkar sufurin jiragen sama musamman a nahiyyar Turai.