✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Barikin Sojin Sama muke bukata a Kafanchan —Sarkin Jama’a ga Buhari

Sarkin ya kuma nemi a sabunta tashar jirgin kasa da ke Kafanchan da kuma babban barikin ’yan sandan kwantar da tarzoma

Sarkin Jama’a Alhaji Muhammad Isa Muhammad II ya bukaci Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya samar da ayyukan ci gaba karkashin Gwamnatin Tarayya a garin Kafanchan, musamman gyara tashar jirgin kasa na garin da ke da girma a fadin Najeriya.

Da yake karbar bakuncin Shugaba Buhari a fadarsa, ya kuma nemi Shugaban Kasar ya gina barikin sojojin sama da na ’yan sandan kwantar da tarzoma na dindindin a garin na Kafanchan tare da sake gina babbar kasuwar garin a matsayinta na cibiyar kasuwanci a yankin Kudancin Jihar Kaduna.

Kudancin Jihar Kaduna dai na daga cikin yankunan da ke fama da matsalar tsaro, da suka hada da ’yan bindiga masu garkuwa da mutane domin karbar kudin fansa da kuma rikicin kabilanci da suka yi sanadiyyar rasa rayuka da asarar dukiyoyi masu dimbin yawa.

Buhari ya ziyarci basaraken ne jim kadan bayan ya kammala bude wasu tituna guda uku a garin, wadanda Gwamna Nasir El-Rufai na Jihar Kaduna ya kammala daga cikin hanyoyi 21 da gwamnatin jihar take gyara a cikin garin Kafanchan da ke Karamar Hukumar Jama’a.

Sarkin ya nuna godiyar al’ummarsa ga shugaban kasa da ya bude titunan, sannan ya yaba wa Gwamna El-Rufai kan ayyukan ci gaba da ya kawo Masarautar Jama’a.

Buhari ya bude titunan da El-Rufai ya gina a Kafanchan

A ranar Alhamis ne dai Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bude wasu hanyoyi guda uku da aka kammala daga cikin hanyoyi 21 da Gwamnatin Jihar Kaduna karkashin Gwamna Nasir Ahmad El-Rufai take ginawa a cikin garin Kafanchan da ke Karamar Hukumar Jama’a da ke yankin Kudancin jihar.

A yayin da yake bude Titin Gidan Sarki, shugaban kasar ya jinjina wa Gwamna El-Rufai bisa kokarin da yake yi na gyara manyan biranen jihar.

Buhari ya kuma yi alkawarin ci gaba da kirkiro da shirye-shiryen da za su amfani ’yan Najeriya.

Da yake nasa jawabin tunda farko, El-Rufai ya ce tituna 21 da yake gyarawa suna daga cikin kashi na farko karkashin shirin mayar da jihar Kaduna sabuwa da ya bullo da shi.

Bayan kammala bude titin ne Shugaban Kasa ya wuce zuwa Fadar Mai Martaba Sarkin Jama’a Alhaji Muhammad Isa Muhammad II.

Sarkin ya nuna godiyar al’ummarsa ga shugaban kasa da ya bude titunan, sannan ya yaba wa Gwamna El-Rufai kan ayyukan ci gaba da ya kawo Masarautar Jama’a.

A watan Nuwamban shekarar 2020 ne Gwamnatin Jihar Kaduna ta bayar da kwangilar gina tituna 21 masu tsawon kilomita 26.3 a kan Naira biliyan 12 ga kamfanonin Farmtrac Nigeria Limited da kuma  Rafali Nigeria Limited.

Jama’a da dama da Aminiya ta zanta da sun yi maraba da zuwan shugaban kasa tare da bayyana farin cikinsu da irin ayyukan raya birane da gwamna El-Rufai yake yi a garin da sauran sassan jihar baki daya.

Titunan da aka bude sun hada da Layin Danhaya da Layin Katsina da Titin Fadar Sarkin Jama’a.