✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Barka da Sallah: Atiku ya bukaci a zauna lafiya

Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa ya bukaci a koma ga Allah

Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar ya bukaci ’yan Najeriya, musamman Musulmi, su karfafi zaman lafiya da hadin kai yayin bikin Sallah Karama.

Sakon Sallar da ya fitar a ta ce zaman lafiya na samuwa ne ta hanyar kauna da hakuri ba ta hanyar kiyayya ko zubar da jini ba.

Atiku ya ce mahimmancin Sallar bai ai takaita ga kammala wajibai a cikin watan Ramadan ba, ya hada da fadakar da tunatar da kai koyaushe don yin tsayin daka domin samuwar neman zaman lafiya.

“Karamar Sallar bana zuwa ne a lokacin da Najeriya ke cikin mawuyacin hali na rahin tsaron rayuka da dukiyoyi baya ga talauci da ke damun mutane.

“A matsayinmu na Musulmi, ya kamata mu tunatar da kanmu game da wajibinmu na tabbatar da zaman lafiya da hadin kai a tsakanin iyalai da makwabta a koyaushe.

“A yau, a fadin Najeriya, akwai tsoro da kuma saurin nuna rashin yarda da juna ta hanyar kabilanci da addini,” inji shi.

Ya ce , babu wata kabila jinsi da ya fi wani sai wanda ya fi tsoron Allah, “Don haka a matsayinmu na Musulmi, dole ne mu dan yi tunani yayin bikin.”

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya yi wa dukkanin Musulmin barka da Sallah tare da addu’ar Allah Ya karbi ibadunsu.

“Da bisa umarnin Allah Madaukakin Sarki ne muka dauki Azumi a cikin Watan Ramadan mai alfarma.

“Bayan cika umarnin, ina taya ’yan uwana Musulmai maza da mata a Najeriya da ma duniya baki daya murnar kammala azumin Ramadan,” inji shi.