✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Basaraken Filato ya kubuta daga hannun ’yan bindiga

’Yan bindigar sun fasa gidan basaraken sannan sannan suka yi awon gaba da shi a ranar Lahadi.

Mai Garin Gindiri na Karamar Hukumar Mangu ta Jihar Filato, Charles Mato Dakat da ’yan bindiga suka sace ya kubuta daga hannunsu.

Kakakin ’yan sandan jihar, ASP Ubah Gabriel, ya tabbatar wa Aminiya hakan a ranar Juma’a.

Maharan sun yi awon gaba da Mista Dakat ne da sanyin safiyar ranar Lahadi.

Wani daga cikin iyalan basaraken ya ce sai da ’yan bindigar suka fasa katangar gidan, sannan suka fasa tagar dakinsa suka yi awon gaba da shi.

Daga baya ’yan bindigar sun tuntubi iyalan basaraken neman neman a ba su kudin fansarsa Naira miliyan 500.

Sai dai babu wani cikakken bayani da ya nuna an biya wasu kudade kafin a sako shi.