✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Bashi hakkin dan Adam ne – Farfesa Yunus

Farfesa Muhammad Yunus, mai bankin Talakawa na Grameen, ya bayyana wa manema labarai cewa bashi hakkin dan Adam ne, a ba shi, ko ba shi…

Farfesa Muhammad Yunus, mai bankin Talakawa na Grameen, ya bayyana wa manema labarai cewa bashi hakkin dan Adam ne, a ba shi, ko ba shi da kama-sayar, wadda za a yi garkuwa da ita.

Farfesa Muhammad Yunus, mashahurin masanin tsimi da tanadi ne, wanda ya samu karramawar lambar yabo ta Nobel a shekarar 2006, ya yi hira da jaridar Gulfnews, inda ya bayyana wa wakilinta yadda ya yi kokarin cim ma muradun karni, tun ma kafin a kirkiro manufar a Majalisar dinkin Duniya.
“Babban Sakataren Majalisar dinkin Duniya ya gayyace ni, don in zama mai fafutikar cim ma muradun karni, kuma ina ganin wannan aiki ne mai matukar muhimmanci, don kyautata rayuwar al’ummar duniya. Aikina a nan shi ne, in yi kokarin ganin an fitar da al’ummar duniya daga kangin talauci.
“Fafutikar da na yi a kasar Bangladesh, duk na yi ta ne wajen bunkasa kananan basussuka da kyautata zamantakewar matalauta, musamman mata. Kuma an tabbatar da cewa, za a iya dabbaka dabarunmu a daukacin fadin duniya,” inji shi.
A hirar da ya yi da jaridar ta Gulfnews, an bijiro masa da al’amuran da suka shafi siyasar duniya, musamman rushewar bangon Berlin (shekara 25 da suka gabata), bangon da ya kange tsakanin Gabashi da Yammacin kasar Jamus, inda ya bayyana cewa, al’amari da ke nuni da cewa akwai bangwayen da suka katange al’ummomin duniya, kuma za a rusa su, ba tare da an harba ko harsashi guda ba.
Ya ce, bango na iya zama na talauci ko na rashin aikin yi, don haka sai a yi aiki tukuru wajen ganin an rusa irin wannan bango.
Da aka bijiro masa da tambaya kan cewa, yaya aka yi ya cim ma manufarsa ta yaki da fatara da talauci, ta hanyar bayar da kananan basussuka, ya ce, “kowane dan Adam na da irin basirarsa, ni kuwa na yi amfani da karamin bashi wajen gwada irin tawa. Kuma na damfaru da tunanin cewa ba shi hakkin dan Adam ne. Na fahimci cewa mutane za su iya samar wa kansu aikin yi idan suka samu bashin jarin yin sana’a.
“Idan har muka wadata su da bashin da za su sana’a, za su samar da abinci da ruwan sha, uwa–uba su ilimantu, tare da kula da lafiyarsu,” inji shi.
An cimma da yawa daga cikin kudurorin muradun karni, inda a halin yanzu duniya ke kokarin rage karsashin talauci. Kuma kasar Bangladesh ita ce babbar abin doka misali. Manufar dai ita ce a rage yawan talauci da kashi 29 cikin 100 nan da shekarar 2015.