✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bashin da ake bin Najeriya ya doshi Naira tiriliyan 34

“Duk da cewa bashin da ake binmu zai yi tashin gwauron zabi, amma duk da haka bai taka kara ya karya ba,” inji shi.

Yawan bashin da ake bin Najeriya ya tashi daga Naira tiriliyan 33 zuwa 34 bayan amincewar Majalisar Dokoki ta Kasa ga Gwamnatin Tarayya kan ciyo karin sama da Naira tiriliyan daya daga kasashen ketare.

A ranar Alhamis ne dai Majalisar Wakilai ta amince da bukatar Gwamnatin na karbo rancen Dala biliyan daya da rabi (kwatankwacin N571.5bn) da kuma Yuro miliyan 995, mako daya bayan Majalisar Dattawa ita ma ta amince da bukatar hakan.

A watan Maris din da ya gabata, Ofishin Dake Kula da Basussuka na Kasa (DMO) ya ce bashin da ake bin Najeriya a iya watan Disambar 2020 ya haura Naira tiriliyan 32.915, wanda Gwamnatocin Tarayya da na Jihohi da ma Babban Birnin Tarayya Abuja suka ciyo.

Kamar yadda Kwamitin Kula da Basussuka na Majalisar ya nuna, za a karbo basukan ne daga Bankin Duniya da kuma Bankin Shige da Fice na kasar Brazil wadanda za a yi amfani da su wajen yaki da annobar COVID-19.

Da yake gabatar da rahoton, shugaban kwamitin a Majalisar ta Wakilai, Hon. Ahmed Dayyabu Safana ya ce za a yi amfani da kudaden ne wajen aiwatar da wasu manyan ayyuka na Gwamnatin Tarayya.

Ya ce, “Duk da cewa bashin da ake binmu zai yi tashin gwauron zabi, amma duk da haka bai taka kara ya karya ba in aka kwatanta shi da karfin tattalin arzikinmu. Muna bukatar karin bashin domin farfado da tattalin arzikinmu,” inji shi.

Da yake tsokaci a kan lamarin, wani masanin tattalin arziki kuma tsohon shugaban Cibiyar Cinikayya, Ma’adinai da Masana’antu ta Abuja, Tony Ejinkeonye, ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta tabbata ta yi amfani da kudaden ta hanyar da ta dace.

Sai dai ya koka kan yadda ya ce bashin na dada karuwa a kullu yaumun, inda ya shawarci gwamnatoci da su fi mayar da hankali wajen lalubo sabbin hanyoyin tara kudaden shiga fiye da na ciyo bashi.

“Dole mu inganta masana’antunmu. Muna bukatar ayyukan raya kasa wadanda za su kawo mana kudaden shiga a kasa,” inji masanin.