Daily Trust Aminiya - Bashin da muke bin Shugaba Buhari
Subscribe

Shugaban Kasa Muhamamdu Buhari

Bashin da muke bin Shugaba Buhari

A yau ma mun bayar da aron filinmu ga Alhaji Abdulkarim Daiyabu, (08060116666, 08023106666), Shugaban Rundunar Adalci ta Najeriya (MOJIN), tsohon Shugaban Jam’iyyar AD na Kasa, kuma tsohon Shugaban Kungiyar ’Yan Kasuwa da Masu Masana’antu da Ma’adanai da Ayyukan Gona ta Jihar Kano, inda ya yi tsokaci kan halin da kasar nan take ciki kamar haka:

Akwai masu zargin cewa surkulle aka yi wa Shugaban Kasa Muhammdu Buhari ya gaza tabuka abin da aka tsammaci zai yi, har ta kai ga ya danka wa wadansu ’yan uwa da abokansa ikon gudanar da aikinsa, suna yin yadda suka dama, tun ana satar kudi har ta kai ana satar mutane. Yanzu dai komai ya zo karshe kowa ya gane wadansu ne suke mulkin Najeriya ba Shugaba Muhammadu Buhari ba. Kuma yadda suke gudanar da mulkin komai kiyayyarsu da mu iyakar zaluncin da za su yi mana ke nan, idan ba so ake sai kowa ya mutu ba.

Mun zabi Shugaba Muhammadu Buhari ne ya jagorancin kasar nan saboda a baya mun ga ya iya gina matatar mai cikin kasa da shekara uku lokacin da yake Ministan Mai a karkashin wani Shugaban Kasa, amma abin takaici yanzu da yake shi ne Shugaban Kasa, shi ne Ministan Mai sai ga shi ya kasa gyara koda matatar mai daya a tsawon shekara hudu da rabi yana mulki. Don haka muna bin sa bashi kan ya hanzarta kawo gyara a kasar nan a sauran watannin da suka rage masa!

An sha sukarsa da cewa yana kewaye ne da wani gungun mutane ’YAN HANA RUWA-GUDU da ake kira KABAL (CABAL) da Ingilishi. Idan haka ne muna rokon  Allah Ya yi mana maganin kabal  da duk wadanda suka jefa mu a irin wannan yanayi.

A yanzu a Najeriya muna hako gangar mai fiye da miliyan biyu na gurbatacce mai a kowace rana, muna da matatun mai dirka-dirka guda hudu, amma abin haushi sai an fitar da da gurbataccen mai zuwa wata kasa an tace sannan a dawo mana da shi a sayar mana da muguwar tsada saboda kudin dako na fitarwa da na dawowa. Bayan kudin tace mai da tsada duk a hada mana mu biya dole.

Wani abin takaicin yayin da Saudiyya ke tace mansu a kan Dala biyar kowace ganga daya, mu a Najeriya a kan Dala 20 ake tace ganga guda. Don me za a ki gyara mana matatun namu mu huta da kudin dako na fitarwa da dawowa da asarar dangogin man fetur din (bye products).  Su ma idan har muna bukatarsu sai mun saya da bala’in tsada. Na sha fadi babu dalilin da za a rika shigo da fetur kasar nan bayan muna da matatu guda hudu.

Babbar masifar ma ita ce hakan na ci gaba da faruwa ne a daidai lokacin da talakan kasar nan ke fama da rashin hanyar samu abin rayuwa saboda rashin aikin yi da rushewar sana’o’in da muka gada iyaye da kakanni da rufe masana’anti da kamfanoni.

Kamar yadda na sha fadi, abubuwa hudu ba su da amfani a Najeriya: arzikin kasarmu ba ya da amfani. 2, mutanen kirki ba su da amfani. 3, ilimi ba ya da amfani. 4, hankali ba ya da amfani. Da ana ana yin amfani da su ba za mu shiga masifun da muke ciki a yanzu ba!

Masu rudar wawayen cikinmu cewa yawanmu shi ne matsalar tattalin arzikin Najeriya, idan ba sa aunawa da irin kazamar satar da manyan shugabanni suka yi, kuma suke ci gaba da yi, mu da suke yi wa sata da kisa ba za mu taba mantawa ba, kuma ba za mu yafe ba.

Duk duniya sun ji yadda barayin shugabanni suka rabe arzikin kasarmu a tsakaninsu da rijiyoyin mai da bankuna da sauransu. Suna boye kudi, biliyoyin dalolin Amurka a ramukan bayi da cikim silin da makabartu da gonaki. Ina jiragen sama da kasa da ake da su yanzu ba ko daya? Sauran kadarori da kamfanoni da masana’antu na gwamnati suna ina?

Tsada masifa ce ga al’umma amma karama ce a kan rashin aikin yi. Mun wayi gari kusan duk sana’o’in hannu da aka sanmu da su a Najeriya sun mutu ko an kashe su da gangan, bayan kuma an rusa masana’antunmu da kamfanoninmu saboda rashin wutar lantarki da ruwan famfo wadanda har kiwon lafiya da tsaro abin ya shafa. Ba a maganar ilimi ballantana aikin ofis na gwamnati ko kamfani. Ga shi an sayar da kadarorin gwamnati ba mu san nawa aka sayar da su ba balle abin da aka yi da su, sai ciwo bashi da ake ta yi da sunan Najeriya babu hanyar biya sai kururuwar barayin shugabanin kasa da jami’an tsaro da alkalai da manyan ma’aikata har da fadar Shugaban Kasa. Ta ina za a fara gyara?

Duk wanda ya sace mana Dala miliyan 100 zuwa miliyan dubu, hakika ba ya tsoron Allah, ba ya tausayin bayin Allah, ba ya da amfani gare mu. Idan gwamnati ta kasa kwato mana wannan dukiya ba ta yi mana adalci ba.

Ya kamata talakwan Najeriya su tuna dabba ce kadai take zuba ido a yanka ’yan uwanta tana tsaye har a zo kanta a yanka. Don haka tunda mu ba dabbobi ba ne, ya kamata mu dauki matakin magance wannan matsala cikin ruwan sanyi, mu bijire wa zaben shugabanni don dan abinda za su ba mu da bai wuce kashe kishin wuni ba.

Sannan su kuma shugabannin da suke kan mulki su tabbatar dukkan wadanda suke rike da kowace amana tamu da wadanda suka taba rikewa a baya kowa ya zazzage kansa da kansa, ko a zazzage shi, gida da waje ya dawo ko a kwato duk abin da ya mallaka ba bisa ka’ida ba.

Dukkan kadarorin gwamnati da suka saye su dawo wa gwamnati da su, duk kudin da aka dawo da su a fara da tallafa wa talakawa masu tsananin bukata da abinci da magani da sutura, sannan a farfado mana da sana’o’inmun na hannu, a inganta su su tafi da zamani ta yadda kowa zai samu aikin yi ya dogara da kansa, wannan ne zai tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali da ci gaba a kasa.

Jami’an tsaro da alkalai da sauran manyan ma’aikata, masu yin dokoki da masu zartarwa da sauransu duk a yi musu garambawul a kori na kora, a tsige na tsigewa, a daure na daurewa, a rataye na ratayewa, a harbe na harbewa. Kasar nan ta gaji da muguwar ta’asar da ake tafkawa saboda an hau kujerar mulki wadda amana ce. Kasar nan ta gaji da jinin da ake zubarwa da sunan addini ko kabila ko bangaranci ko satar dabbobi da garkuwa da mutane.

Kuma wajibi ne mu tabbatar duk wanda za a zaba ko aka nada sai ya zama dan kasa nagari ne wanda ba barawo ba, ba fajiri ba, ba dan kungiyar asiri ba. A yi haka koda zai kai ga sabunta Kundin Tsarin Mulkin kasar nan ne, ta yadda za a kiyaye rayukanmu da lafiyarmu da dukiyarmu da mutuncinmu da imaninmu kamar yadda Allah Mahaliccin kowa da komai Ya yi umarni a rika gudanar da mulki ko’ina a duniya.

More Stories