✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bashin N100bn: APC ta zargi Finitiri da wawure kudin jama’a

Gwamna Fintiri ya ce ’yan adawa ne ba su fahimci yadda abin yake ba.

Ana ci gaba da ce-ceku-ce kan shirin Gwamnatin Jihar Adamawa na karbo rancen Naira biliyan 100.

Gwamnan Jihar, Alhaji Ahmadu Umaru Fintiri ya ce za a yi amfani da kudin ne wajen gyara kasuwannin dabbobi da na hatsi don inganta samun kudin shiga ga jihar.

Tuni Jam’iyyar APC mai adawa ta ce dabara ce ta wawure kudin al’umma.

A wata hira da BBC, Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri ya ce ya zama dole a samo sababbin hanyoyin samun kudin shiga domin rage dogaro kan Gwamnatin Tarayya da kuma kudin mai.

Tun a lokacin da Gwamnan ya sanar da cewa gwamnatinsa za ta karbo rancen aka fara tayar da jijiyoyin wuya a tsakanin bangaren gwamnati da na ‘yan adawa a jihar.

Gwamnati na cewa wata sabuwar hanya ce ta samun kudin shiga ta gano, su kuwa ’yan adawa cewa suke yi wata hanya ce ta yin sama da fadi da kudaden al’umma.

Gwamna Fintiri ya ce ’yan adawa ne ba su fahimci yadda abin yake ba.

“Mutane ne wadanda ba su gane yadda tsarin yake ba.

“Idan kuma an dauki bashi bisa wannan tsarin, tsarin nezai haifar da kudi da za a biya wannan bashin da shi, don haka babu laifi” a cewar gwamna Fintiri.

“A yanzu wa zai ba ka kudi cikin duhun kai? Bari in gaya maka, duk sa daya da ya bar Mubi yaje Jihar Legas ya hau kan kwata, aka yanka, dubu goma Legas ke karba, saboda haka a shekara daya Jihar tana samun biliyan 27 daga shanu da ke shiga cikinta daga garin Mubi da ke Jihar Adamawa.

“Gaya mini idan muka fara wannnan harkar a Adamawa muka samu wadannan kudaden asara muka yi?”

Abin da ’yan adawa ke cewa Tun bayan sanar da batun karbo rancen jam’iyyar adawa ta APC a jihar ta fito ta yi fatali da shi.

APC na ganin gwamnati na yunkurin wawure kudaden da ta ce za ta karbo ne.

Mukaddashin sakataren jam’iyyar a Adamawa Mista Wafari Theman ya ce wannan ba shi ne lokacin da ya fi dacewa a karbo rance ba ganin cewa ta kashe kudade sama da Naira biliyan takwas wajen gina gadar sama.

“Yaya gwamnati za ta binne biliyoyin Naira a cikin siminti wanda ba ya kawo amfani sannan kuma ta ce za ta je ta karbi rance a kan riba don inganta noma, me ya sa ba ta yi amfani da kudin da aka binne wajen yin noma ba tuntuni?

“Su waye ne wadanda za suyarda su zuba jarin? Wa ka ga ya shigo ya ce zai saya? Me suka gani a kasa? Ai akwai hatsari a cikin wannan abin,” inji Mista Wafari.

Su ma al’ummar jihar ra’ayoyinsu sun kasu kashi uku kan wannan batun, a yayin da wasu ke ganin abu ne da zai taimaka mata ta farfado wasu kuwa na ganin ba lallai ne a yi amfani da kudaden ta yadda ya dace ba, sai kuma ’yan tsakatsaki masu jiran ganin yadda shirin zai kaya.

Don ganin yadda karbo rancen zai inganta kasuwannin dabbobi da kuma hatsi da ke garuruwan Mubi da Ganye da Ngurore da Cigari da sauransu.