✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bassa/Jos ta Arewa: An fara jefa kuri’a a zaben cike gurbi

Mutane sun fara jefa kuri’a tun da misalin karfe 8 na safe a zaben cike gurbin dan Majalisar Wakilai mai wakilitar kananan hukumomin Bassa da…

Mutane sun fara jefa kuri’a tun da misalin karfe 8 na safe a zaben cike gurbin dan Majalisar Wakilai mai wakilitar kananan hukumomin Bassa da Jos ta Arewa na Jihar Filato.

Zaben na gudana ne a ranar Asabar bayan rasuwar dan majalisa mai wakiltar kananan hukumomin biyu.

Wakilinmu ya zaga wasu rumfunan zabe da ke gundumar Naraguta Ward “B” inda ya iske jami’an zabe sun isa wurin da kayan zabe a kan lokaci.

Masu zabe sun fito kada kuri’arsu domin su zabi wanda zai ci gaba da wakiltar su a Majalisar Tarayya.

A zagayen da wakilinmu namu ya yi a safiyar Asabar, ya samu an tsaurara matakan tsaro a daukacin rumfunan zabe da ke Karamar Hukumar Jos ta Arewa.