✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Bata-gari 45 sun fada komar ’yan sanda a Delta

Rundunar ’yan sanda a Jihar Delta, ta ce ta kwato bindigogi kirar AK47 guda biyar daga hannun wasu miyagu da ta damke wadanda na wasu…

Rundunar ’yan sanda a Jihar Delta, ta ce ta kwato bindigogi kirar AK47 guda biyar daga hannun wasu miyagu da ta damke wadanda na wasu jami’anta da aka kashe ne a kwanan baya.

Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar, Muhammed Ali ne ya bayyana haka a lokacin da rundunar ke holen wasu da take zargin masu aikata manyan laifuka ne su 45 da jami’anta suka kama.

An kama ababen zargin ne kan laifukan da suka hada da fashi da makami, harkokin kungiyar asiri, garkuwa da mutane, fyade, sayar da jarirai da sauransu.

Da yake yi wa manema labarai bayani game da wadanda ake zargin, Kwamishinan ya ce “Wadannan bindigogi kirar AK-47 da aka kwato daga ‘yan ta’addan na jami’anmu ne. Sun kashe mana jami’ai sannan suka kwashe bindigoginsu.”

Ali ya kara da cewa, daga cikin wadanda aka cafke din har da wasu mutum uku da ake zargi da kashe wani Isaac Odubu da matarsa a kauyen Amai, wanda kafin kashe matar sai da suka yi mata fyade.

Ya ce bayan kammala bicikensu, za a gurfanar da duka wadanda ake zargin a kotu don su fuskanci shari’a.