✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Bata-gari sun cinna wa ofishin INEC wuta a Kano

Ana fargabar rikicin da ya barke a ofishin INEC ya yi ajalin mutum hudu

Wasu bata-gari da ba a gano ko su wane ne ba sun cinna wa ofishin INEC na karamar hukumar Takai wuta.

Wani ganau da ya nemi a sakaya sunansa ya ce lamarin ya faru ne da safiyar ranar Lahadi, bayan wani rikicin magoya bayan jam’iyyau ya balle.

Ya kuma ce an samu nasarar kashe wutar, kafin tayi ta’adi, amma “Duk da haka wasu sun samu rauni suna ma asibiti suna karbar magani, hudu kuma sun mutu.”

Rahotanni na nuna rikicin ya fara ne, yayin tattara sakamakon zaben karamar hukumar.

A nasa bangaren Kakakin rundunar ’yan sandan jihar SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya tabbatar da faruwar lamarin, ya kuma ce a dakin ajiye janareta aka cinna wutar, sai dai an samu kashe wa tun ba ta yi nisa ba.

Sai dai ya ce ba shi da masaniyar asarar rai ko daya.