✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bata-gari sun kwakule idon almajiri a Bauchi

Sun yaudari dan almajirin ne suka dauke shi zuwa gefe gari inda suka kwakule masa idon.

Wasu bata-gari da ba a san ko su wane ne ba, sun kwakule idon wani almajiri a Jihar Bauchi.

Jaridar Punch ta rawaito cewar, lamarin ya faru ne a garin Kafin Madaki, hedkwatar Karamar Hukumar Ganjuwa da ke jihar.

Mai magana da yawun Rundunar ’Yan Sandan Jihar, Ahmed Wakil, ya tabbatar da faruwar hakan cikin sanarwar da ya fitar ranar Talata.

Majiyarmu ta ce, yaron da lamarin ya shafa mai shekara 12, an kai shi Bauchi daga Kano ne don yin karatun Alkur’ani.

Wakil ya ce, Kwamishinan ’Yan Sandan jihar, Aminu Alhassan, ya ba da umarnin zurfafa bincike don kamo wadanda ke da hannun a aika-aikar.

Ya kara da cewa, bata-garin sun zo ne a kan babur inda suka yaudari yaron suka dauke shi zuwa wani gida da nufin ya kira musu wata budurwa.

Ya ce, daga nan sai suka tafi da shi zuwa wani kebabben wuri a gefen gari.

Jami’in ya ce, bayan raba shi da idonsa daya sai suka yasar da yaron, inda daga bisani ya lallaba zuwa inda jama’a suka tsince shi jikinsa sharkaf da jini.

Daga nan aka ce an dauki yaron zuwa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi, bayan da aka kai wa ’yan sandan yankin rahoton abin da ya faru.