✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Batanci ga Annabi: Shugabannin Musulman Indiya sun bukaci dakatar da zanga-zanga

Shugabannin addini sun ce zanga-zangar na iya zama cin zarafi

A daidai lokacin da ’yan sandan Indiya ke tsammanin zanga-zanga bayan idar da sallar Juma’a [gobe] kan batanci ga Annabi Muhammad (S.A.W), malamai a kasar sun bukaci Musulmi su mayar da wukakensu cikin kube.

Ana tsammanin za a yi zanga-zangar ce bayan Sallar Juma’a don neman a hukunta tsohuwar kakakin jam’iyyar BJP mai mulkin kasar, Nupur Sharma, saboda batancin.

Sai dai malamai da shugabannin addinin Musulunci a biranen kasar da dama sun yi kira ga Musulman kasar da su hakura da zanga-zangar don gudun cin zarafinsu.

A Juma’ar makonni biyun da suka gabata dai, Musulmai da dama sun yi zanga-zangar neman a hukunta Nupur din.

Sai dai a wasu wurare da dama, zanga-zangar ta rikide zuwa tarzoma, inda aka rika yin taho-mu-gama tsakaninsu da ’yan sanda, a ranakun uku da 10 ga watan Yuni.

Ba mu da kudin karbo belinku — Syed Ahmed Bukhari

A cewar Syed Ahmed Bukhari, Babban Limamin masallacin birnin Delhi, ya kamata mutane su sa ido kan masu kokarin tayar da zaune tsaye ta hanyar fakewa da zanga-zangar.

Ya ce, “Za a iya kaucewa mummunar zanga-zangar da ta faru a kasar nan a makon da ya gabata, ya kamata mutane su nemi izinin ’yan sanda kafin su fara ta.

“Zagin Annabi (S.A.W) dole zai yi wa dukkan Musulmin kwarai ciwo, amma ba haka ya kamata a yi zanga-zangar ba. Ba daidai ba ne a saka yara da matasa a ciki.

“Mutane sun rika jifa da duwatsu, su kuma ’yan sanda suka bude musu wuta, har suka kashe matasa biyu, wasu da dama kuma aka raunata su,” inji limamin.

Ko a makon da ya gabata, Musulmin Indiya sun zargi hukumomin Indiya da rushe gidajen wasu da suka fita zanga-zangar a sassan kasar.

Kasashe da kungiyoyin Musulmai a fadin duniya dai na ci gaba da Allah-wadai da batancin, inda wasu daga cikinsu suka shirya zanga-zangar kin jinin matakin a kasashensu.