✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rufe masallaci: Sheikh Abduljabbar ya yi raddi ga Gwamnatin Kano

Malamin ya ce yi bakin zalunci ne kuma da gangan gwamnatin ta rufe masallacin.

Fitaccen malamin Musulunci a Jihar Kano, Sheikh Abduljabbar Sheikh Nasiru Kabara ya ce ‘zalunci’ rufe masallacinsa da majalisinsa da Gwamnatin Jihar Kano ta yi bisa zargin sa da yin batanci ga Sahabban Manzon Allah (SAW) da tunzura jama’a.

Malamin ya mayar da martani ne ’yan sa’o’i bayan Gwamantin Jihar ta sanar da matakin tare da haramta masa gudanar da karatuttuka ko gabatar da lacca ko ko huduba ko sanya karatuttukansa a kakafen yada labarai har sai an kammala bincike.

Sheikh Abduljabbar wanda malamai a jihar ke sukar da’awarsa da cewa tunzuri ne da kuma batanci ga Sahabbai ya ce da gangan gwamnatin jihar ta yi abin da ta yi masa, wanda ya ce ramuwar gayyar siyasa ce.

“Mai son ya san gwamnati ta san zalunci ta aikaita, zalunci bakin kirin wanda babu dalili kan yin sa ya nemi hirar da Kwamishinan Ilimi ya yi a daren jiya.

“Za a ji yana fada karara, wadannan malamai da gwamnati jiya ta dafa wa, tana da cikakkiyar masaniya cewa azzalumai ne, marasa gaskiya ne, masu siyasar addini ne, kuma sun juya al’amura ne da gangan,  sun shigar da siyasa ciki sabanin ilimi.

“Wannan za a ji a hirar da Kwamishinan Ilimi ya yi a daren jiya, kafin su saki wannan sanarwar; Ya yi wannan maganar kuma da yawun gwamnatin ya yi ta. Don haka bayanan da ya yi a daren jiya su ne amsa ga gwamnati bisa hukuncin da ta yi a daren jiya,” inji shi.

Game zargin karatuttunkansa da tunzura jama’a da malamai suka yi, malamin ya kalubalanci gwamnatin da ta yi bincike, ba ta kama shi da laifi kan abin da ba ta ta cikakken masaniya a kai ba sabdoa malamai masu kusanci da ita sun kawo mata.

“Ta yaya gwamanti ta san wannan? Gwamnati ta san iliman addini? Gwamnati ta san wadannan litattafi da nake ciro mangaganu? Gwamnati ta yi bincike ta duba su ta ga maganganun nan babu su, ni na fada ya zama na tunzura jama’a?

“Ya kamata gwamnati kafin ta lisafta min maganganun ta tabbata ni na yi su.

“Idan kuma akwai su a litattafai ba ni na yi ba to gwamnati ta zalunce ni ke nan, don maganganun ba nawa ba ne, na wadanda da suka rubuta ne, ban ga laifi ba don na bijirar da su,” inji shi.

An girke jami’an tsaro

Tuni dai aka girke jami’an tsaro kofar gidan malamin da ke unguwar Gwale a birnin Kano.

Akalla motocin jami’an tsaro biyar ne aka girke a kofar gidan malamin, don tabbatar da bin umarnin da gwamnatin jihar ta kafa masa.

Sai dai Aminiya ta gano  jami’an tsaron ba su hana mabiya da masu jaje ga malamin shiga gidan nasa ba.

Wakilinmu ya ga daruruwan almajiran malamin a wajen gidan da kofar masallacinsa na tururuwar yi masa jaje game da hukuncin da gwamnatin jihar ta dauka a kansa.

‘Malamai ba su da amsa’

Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara, wanda mabiyin Darikar Kadiriyya ne, wasu malamai daga ciki da wajen jihar na ganin ya sauka daga layin koyarwar jamhurin Shugabannin Musulunci.

A tattunawarsa da Sheikh Abduljabbar ya ce matakin da gwamnatin ta dauka a kansa ya tabbatar masa da cewa a kan gaskiya yake, kuma malaman da ke zarginsa da kagen karatu ba su da abin fada.

“In da abin da na ji shi ne tabbatatar kasancewata bisa gaskiya, domin ba da gwamnati nake magana ba da malamai nake; ya zama karshe gwamnati ce ta amsa musu, wannan sai ya nuna mini malamai ba su da amsa.

“A matsayina na almajiri, maganar da nake yi ta ilimi ce da malamai, ya zama mai ban amsa ita ce gwamnati ce take amsa musu, ya nuna malamai ba su da amsa,” inji malamin.