✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abduljabbar zai kara zaman mako uku gidan yari

Kotu ta dage sauraron shari'ar zuwa 18 ga watan Agusta mai kamawa.

Babbar Kotun Shari’ar Musulunci da ke zamanta a Kofar Kudu a Jihar Kano ta dage sauraren shari’ar Abduljabbar Kabara zuwa ranar 18 ga Agusta 2021.

Alkalin kotun Mai Shari’a Ibrahim Sarki Yola, ya kuma ba da umarni a ci gaba da tsare Abduljabbar a gidan yari, duk da cewa ya musanta zargin da ake masa.

An gurfanar da Abduljabbar Kabara, wanda malamin addinin Musulunci ne bisa zargin yin batanci ga Annabi Muhammadu (SAW) da kuma tayar da zaune-tsaye da sauran laifuka.

Abin daya faru a kotu

A zaman kotun na ranar Laraba, mai gabatar da kara, Aisha Mahmud, ta bukaci kotun ta dage zaman domin gwamnatin jihar ta kammala hada bayanai da kuma gabatar da shaidu.

Amma lauyan Abduljabbar ya ce malamin ya shafe kwana 12 a tsare kafin a gurfanar da shi a kotu, saboda haka abin takaici ne masu shigar da kara su ce ba su gama shiri ba a tsawon lokacin.

A cewarsa, hakan alama ce da ke nuna suna so ne su kawo wa kotu tafiyar hawainiya a shari’ar ta Abduljabbar.

Bukatar hujjoji

Saboda haka ya bukaci a ba su sunayen shaidun da adireshinsu da bayanansu da kuma bayanin da Abdujabbar din ya rubuta a ofishn ’yan sanda.

Lauyan na Abduljabbar ya kuma bukaci a ba shi muryoyi da bidiyo da hotuna da sauran hujjojin ake so a gabatar a kotu kafin zaman na gaba.

Mai gabatar da kara ya bukaci kotu ta sauraron shari’ar zuwa ranar 25 ga watan Agusta domin ba su damar kintsawa, sannan ya bukaci kotun ta dage zamanta zuwan ranar 11 ga watan Agusta.

Alkalin kotun ya dage zaman zuwa ranar 18 ga watan na Agusta, ya kuma ba da umarnin a mayar da malamin gidan yari.

Wakiliyarmu ta bayyana cewa Abduljabbar yana cikin koshin lafiya a lokacin da ka aka gurfanar a kotu, sabanin ji-ta-ji-ta da aka yada a baya cewa ya kamu da rashin lafiya a gidan yarin da ake tsare da shi.

Kama Abdulabbar

A ranar 16 ga watan Yuli jami’an tsaro suka cafke bayan Gwamnatin Jihar ta kai karar sa, bisa zarge-zargen da a kansu aka gudanar da mukabala tsakanin Abduljabbar din da wasu malaman Kano.

Bayan mukabalar, alkalinta, Farfesa Salisu Shehu ya sanar cewa Abduljabbar ya kasa amsa tambayoyin da aka yi masa kan mas’alolin da ake zargin sa a kai, sai kame-kame yake yi.

Farfesa Salisu Shehu ya kuma shawarci Gwamantin Jihar Kano da ta dauki matakin da ya dace a kan al’amarin.

Bayan nan ne Abduljabbar ya fito ya nemi afuwar al’ummar Musulmi a wani salo da ake gani a matsayin rashin laifi.

Ana cikin haka ne ’yan sanda suka gayyace shi zuwa ofishinsu, suka kuma tsare shi, Gwamnatin Jihar Kano kuma ta maka shi a gaban kuliya a ranar 16 ga watan Yuli.

Abduljabbar dai ya sha musanta zargin da ake masa na batanci ga Manzon Allah (SAW) da Sahabbai da kuma turzura jama’a.